Ƴar Katsina, DSP Fatima Abdul’aziz ta zama dogarin matar mataimakin shugaban kasa

1
210

Ƴar Katsina, DSP Fatima Abdul’aziz ta zama dogarin matar mataimakin shugaban Ƙasa

Jami’ar ‘Yar Sandar Najeriya, DSP Fatima Abdul’aziz, Yar Asalin Jihar Katsina Ta Zama Babbar Dogarin Uwargidan Zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Kasa, Nana Kashim Shettima.

Jami’ar mai suna Fatima AbdulAziz ‘yar asalin karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina ce kuma tana da

girman Mataimakiyar Sufritandan DSP.

A baya dai wasu kyawawan hotunan jami’ar ya yi ta yawo a kafafen sadarwar zamani.

A bisa al’ada daman, jiga-jigan mutane masu muhimmanci da ake kira da VIPs a turance kamar shugaban kasa da mataimakin sa da matan su da Gwamnoni da ma ministoci da kwamishinoni da dai sauran su sukan samu masu kula da su daga rundunar Ƴan sandan Najeriya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here