Ba mu amince da rabon mukaman APC a majalisa ba – Ahmed Wase

0
78

Mataimakin shugaban Majalisar Wakilai ya gabatar da korafi kan matakin uwar jam’iyyarsu APC, na raba muĆ™aman shugabannin majalisa ta goma ga shiyyoyin Najeriya.

Ahmed Idris Wase da wasu masu neman shugabancin Majalisar Wakilai sun kai takardar korafin ne shalkwatar APC ta kasa da ke Abuja, suna kira ga jam’iyyar mai mulki ta sake nazari kan matsayarta.

Ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a shalkwatar APC, jim kaÉ—an bayan miĆ™a takardar Ć™orafinsu ga shugabancin jam’iyyar game da matakin da ta É—auka.

Matakin nasu na zuwa ne a lokacin da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ke gudanar da wani taron gaggawa a kan rikicin da ya taso game da batun shugabancin majalisar ta 10.

A ranar Litinin ne, APC ta fitar da sanarwa inda ta ce ta amince da raba mukaman shugabannin majalisa ta goma a tsakanin wasu shiyyoyi na Najeriya.

APC ta ce kwamitin gudanarwarta na ƙasa, ya amince da goyon bayan Sanata Godswill Akpabio, a matsayin shugaban Majalisar Dattijai da kuma Tajuddeen Abbas, a matsayin kakakin Majalisar Wakilai.

Masharhanta sun yi hasashen cewa matakin zai Ć™ara tayar da Ć™ura da kuma janyo rarrabuwar kai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar mai mulki da kuma masu neman shugabancin majalisa ta goma.

A ranar Litinin din da ta wuce ma, Ahmed Idris Wase ya ce sun ziyarci taron da Mukhtar Aliyu Betara ya kira a Abuja don ayyana takararsa ta neman shugaban Majalisar Wakilai da za a buÉ—e nan gaba.

A wani saĆ™o da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Ahmed Wase ya ce: “Bisa yarjejeniyar da rukunin masu neman shugabancin majalisar wakilan ya cimma, ya ziyarci takarar da Mukhtar Betara ya Ć™addamar.

Rukunin masu neman takarar dai, kamar yadda mataimakin shugaban majalisar, ya rubuta su ne: Ahmed Idris da Mukhtar Betara da Aminu Jaji da kuma Sada Soli Jibia.

wanda shi ma tuni ya sanar da takararsa

A safiyar Larabar, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu, ya gana da mutanen da APC ke mara wa baya Hon. Tajudeen Abbas da kuma Hon. Benjamin Kalu, a matsayin kakakin da mataimakin kakaki Majalisar Wakilai.

Wata sanarwa da ofishin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya fitar ta ce kwamitin haɗin gwiwa daga Majalisar Wakilai ne ya gabatar da masu neman shugabancin biyu, ga Bola Ahmed Tinubu.

Sanarwar dai ba ta yi Ć™arin haske kan abin da zaÉ“aÉ“É“en shugaban ya tattauna da ‘yan majalisar wakilan biyu da APC ta amince su kasance shugaba da mataimakin shugaban majalisar wakilan ta goma ba.

Bangaren su Ahmed Wase dai ya ce yana fata shugabancin APC zai sauya shawara kan wannan mataki.

Ya kuma ce suna da ƙwarin gwiwa taron da kwamitin gudanarwar APC ke yi a halin yanzu zai saurari kokensu kuma kwalliya za ta biya kuɗin sabulu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here