Kante mai shekaru 32 har zuwa yanzu yaki amincewa da sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita kwantiraginsa wanda ake alakantawa da halin da kungiyar ke ciki, sai dai Chelsea na ganin kawo Pochettino zai bai wa dan wasan na Faransa kwarin gwiwar ci gaba da zama.
A cewar Chelsea sai da ta tattauna da Kante gabanin raba gari da manajojinta 2 da ta kora a baya-bayan nan.
Yanzu haka dai ana tattaunawa tsakanin Pochetttino da Chelsea kuma akwai yiwuwar cimma jituwa cikin makon nan.
Akwai dai alaka mai karfi tsakanin Pochettino da Kante wanda a wancan lokacin ya so daukar dan wasan na tsakiya zuwa PSG a Faransa.
Ngolo Kante wanda ya lashe kofin duniya da Faransa a 2018, ana ganin zai iya ci gaba da zama a Stamford Bridge idan har ragamar horarwar ta koma hannun Pochettino.