Dattawan jihar Katsina sun roƙi gwamna Masari ya daure ya karɓi mukami a gwamnatin Tinubu

0
103

Mai girma gwamnan jihar Katsina, Alh Aminu Bello Masari ya fadi haka a yau lokacin da Kungiyar Dattawan Jihar Katsina Mai suna “Katsina State Elders Forum” suka Kai mashi ziyarar bankwana, a fadar gidan Gwamnati.

Masari ya cigaba da cewa Dikko Umar Radda danku ne, kuma shima dan Jihar Katsina ne yanzu shine wanda zai gaje ni, saboda haka ina rokon ku da ku bashi goyon baya fiye da wanda kuka bani, kana ku rika bashi shawara ba tare da gajiyawa ba , domin ciyar da Jihar Katsina gaba.

Maigirma Gwamna ya cigaba da cewa babu abinda yafi mahimmanci ga Shuganci fiye da mutunta al’umma da sanin darajarsu da kuma ba kowa darajar da Allah S.W.A ya bashi a matsayin mutum, wannan shine kyakyawan shugabanci.

Daga karshe Maigirma Gwamna yayi masu godiya ta musamman akan irin shawarwari da cikakken goyon baya da suka bashi yayin gudanar da Shugabancinshi, haka kuma yayi kira da su kara kaimi wajen hada kan al’ummar Jihar Katsina.

Tun a farko Shugaban Kungiyar Dattawan Alh Aliyu Balarabe wanda Alh Ali Sani Sakataren kungiyar ya gabatar da jawabi a madadin Shugaban, yace babu abinda zamu yi sai yima Allah godiya da ya kawo karshen wannan mulki na Maigirma Gwamna Aminu Bello Masari lafiya, duk da kalubalen da ya fuskanta amma ya samu nasarori masu tarin yawa na inganta rayuwar al’ummar Jihar Katsina.

Ya ce Gwamna Aminu Bello Masari dole a jinjina mashi tare da yaba mashi, abisa ayyukan cigaban kasa da ya shinfida ma Jihar Katsina, kama daga gyaran magudanun ruwa, gyaran makarantu da gina wasu, gyaran asibitoci, samar da cibiyar koyon aikin likitanci,gina hanyoyi, gina gadoji na Kasa da sama guda ukku acikin garin Katsina, samar da ruwan sha, da sauran wasu muhimman ayyukan da lokaci ba zai bari mu ayyana su ba. Yace daga Karshe suna mashi godiya tare da fatan alkhairi a madadin kungiya.

Shima a nashi jawabin Mai Shari’a Sadiq Abubakar Abdullahi Mahuta Kuma Galadiman Katsina, Hakimin gundumar Malumfashi, yace Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Alh Aminu Bello Masari Shugaba ne na gari, kuma abin koyi, wanda bashi da wani buri da ya wuce cigaban al’umma, dan haka ya zama wajibi mu gode mashi , kuma zamu kasance masu yi maka addu’a Allah ya kara daukaka darajarka, kana zamu cigaba da yi maka biyayya.

Shima anashi jawajin Alh Abubakar Danmusa yace Kafin ya marama Masari baya, sai da ya gindaya mashi sharudda guda biyu, na daya zaya gyara masu abisitin Garin Dan musa , na biyu zaya gyara masu makarantar sakandire ta garin Danmusa, yace duk Maigirma Gwamna yace ya dauki alkawari zaiyi, cikin yarda Allah bayan samun nasarar Masari, yau gashi duka alkawurran da ya daukar mani ya cika su, saboda haka da wannan sai mu tayashi murna , muna mashi fatan alkhairi.

ShimaMinista Alh Abu Gidado ya yabama Masari abisa Dattakunshi da karbar shawara da yake yi, haka kuma yace abinda baku sani ba shine duk watan azumi idan ya kama sai ya dauki nauyin ciyar da mutane dari biyar har azumin watan Ramadan ya kare a masallacin Bilal Bin Rabah dake Layout, Allah ya saka mashi da alkhairi.

Haka kuma wasu daga cikin dattawan anasu jawabin sun bayyana Maigirma Gwamna mutum Mai tausayi hakuri da juriya wanda wannan hakurin nashi ne yasa ya samu nasara a mulkinshi, muna mashi fatan alkhairi.

Daga karshe Kungiyar Dattawan ta roki Maigirma Gwamna da cewa Dan Allah idan an bashi mukami a sabuwar Gwamnatin Tarayya to ya yayi hakuri ya karba domin ya cigaba da ba al’ummarshi gudunmuwar da ya saba.

Wadanda suka halarci zaman sune kamar haka: Maigirma Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina QS Alh Mannir Yakubu, Alh Muntari Lawal, Sakataren Gwamnati, Alh Idris Usman Tune, Shugaban Ma’aikata na Jiha, Alh Bature Umar Masari Shugaban Ma’aikata, da wasu daga cikin yan Majalisar Zartarwa, Alh Salisu Mamman Kadandani, CEO Continental Computers, da wasu daga cikin mataimaka na musamman na Maigirma Gwamna.

Daga Ofishin Darakta Janar, Sabbin Kafafen Sadarwa na Zamani na Maigirma Gwamna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here