EFCC ta cafke tsohon ministan wutar lantarki saboda karkata naira biliyan 22

0
112
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeria ta cafke tsohon ministan wutar lantarki Injiniya Saleh Mamman saboda zargin da ake masa na karkata akalar naira biliyan 22 da aka ware domin inganta samar da wutar lantarki a fadin kasar.

Rahotanni daga kasar ciki harda Jaridar Daily Trust sun ruwaito cewar jamiā€™an EFCC sun yi awon gaba da tsohon ministan ne yau laraba, kuma yanzu haka yana can yana amsa tambayoyi akan yadda wadannan makudan kudade suka salwanta.

Bayanai sun ce ana zargin Mamman ne da karkata naira biliyan 22 da aka ware domin aikin samar da wutar Zungeru da Mambilla wanda ake zargin ministan sun raba tare da wasu manyan jamiā€™an maā€™aikatar sa.

Majiyoyi sun ce jamiā€™an EFCC sun yi nasarar gano wasu kadarori a Najeriya da kasashen ketare da ministan ya mallaka tare da wasu tarun kudade da suka kunshi nairori da dalolin Amurka.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Mamman a matsayin minista daga Jihar Taraba a shekarar 2021 da zummar ganin an gina tashar samar da wutar Mambilla amma kuma ya tube shi a watan Satumbar shekarar 2019 saboda rashin gamsuwa da aikinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here