Masana sun cire cutar AIDS daga sahun cutukan da ke barazana ga dan adam

0
111

Shekaru 40 bayan gano cutar sida ko kuma AIDS wani binciken masana ya nuna cewa cutar ta fice daga sahun cutuka masu barazanar kisa sakamakon cin karfinta wajen rage tasirinta da kuma wayar da kan jama’a dangane da matakan kariya baya ga nasarar iya fara warkar da masu dauke ita.

Dai dai lokacin da UNAIDS ke fatan kawo karshen kasancewar AIDS barazanar lafiya nan da shekarar 2030, alkaluman da AFP ta tattara na nuna yiwuwar tabbatuwar wannan fata, bayan jerin nasararoin da aka samu a yaki da cutar.

Alkaluman masana sun nuna cewa cikin shekaru 40 bayan gano cutar zuwa yanzu ta kashe mutanen da yawansu ya kai miliyan 40 da dubu dari 1 duk da cewa ana ganin raguwar masu mutuwa sanadiyyar cutar shekara bayan shekara.

Kwararrun da ke bincike kan cutar ta AIDS ko kuma sida sun bayyana cewa maimakon barazana ko kuma tikitin mutuwa da cutar ta ke a baya, a yanzu ta na sahun manyan cutuka ne da za a iya rayuwa da su.

A watan Yunin 1981 kwararren likita mai binciken cutuka na Amurka ya gano cutar a jikin wani mai auren jinsi can a California a Amurka gabanin bata suna da kuma gano hadari da saurin yaduwarta a 1982 da kuma bayyana ta a matsayin barazana.

A shekarar 1983 kwararrun masu bincike da suka kunshi Francoise Barre-Sinoussi da Jean-Claude Chermann wadanda ke aiki karkashin Luc Montagnier suka gano kwayar cutar HIV wadda ke haddasa cutar ta AIDS.

Nasarar samar da magunguna rage tasirin kwayar cutar na anti-retroviral a shekarar 1987 sun taimaka matuka wajen rage yawan masu kamuwa dama wadan ke mutuwa daga cutar.

Duk da yadda alkaluma ke nuna irin barnar da cutar ta HIV Aids ta yi a shekarun 1990 bayan zama babbar sanadin kisan kisan matasa ‘yan shekaru 25 zuwa 44, amma an samu sassaucinta a shekarun 2000 sakamakon wayar da kai da kuma samar da matakan kariya daga cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here