Mutane 10 ne ake fargabar sun mutu bayan shan shayin da aka yi da ganyen zakami wajen daurin aure a Kano

0
107
Kano

Akalla mutane goma ne ake fargabar sun mutu, wasu da dama kuma suna kwance a asibiti bayan sun sha shayin da ake zargin an dafa shi da wani ganye mai suna ‘zakami’ a wani daurin aure da aka yi a unguwar Sheka da ke jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya.

Zakami, ganyen shayin gargajiya ne mai  ƙunshe da sinadarin psychoactive.

A cewar shaidun gani da ido sama da mutane 50 ne suka sha shayin.

Daya daga cikin wadanda suka shaida lamarin, Sanusi Yahaya, wanda kuma dan uwa ne ga amaryar, ya ce ana zargin shayin da wasu magunguna daban-daban banda ganyen zakamin.

A cewarsa, ya zama ruwan dare ga matasan yankin musamman masu shaye-shayen miyagun kwayoyi, wajan dafa shayi a lokacin bukukuwa kuma su kan fake a karkashinsa su sha kwaya, inji rahoton Aminiya.

“Sun dafa shayin kuma su da kansu ba su san adadin da nau’in magungunan da ke ciki ba har wasu sun watsar da shi. 

Amma wasu daga cikinsu sun dage cewa dole ne su sha shayin, suna masu cewa kwakwalwar su na iya dauka.

“Bayan shan shayin , mutane biyu sun mutu, wasu sun murmure yayin da wasu ke kwance a asibiti,” in ji shi.

Wani da abin ya faru a gabansa Abdullahi Muhammad ya ce ya zuwa ranar Talata mutane bakwai ne suka mutu.

Ya ce wasu daga cikin wadanda ke kwance a asibiti ba ’yan unguwar ba ne amma suna wucewa ne kawai suka yanke shawarar shan shayin.

“Ba mu san ainihin adadin ba a yanzu, amma da safe an tabbatar da mutuwar mutane bakwai. Wasu ma ba a gayyace su zuwa daurin auren ba, sun zo ne domin su yi kwalliya su sha kwaya,” inji shi.

An kasa samun damar jin ta bakin angon domin jin ta bakinsa game da lamarin saboda an ce ya gudu tare da wasu abokansa.

Kokarin jin martani daga kakakin rundunar ‘yan sandan Kano , SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ci tura saboda ba a iya samun lambar sa.

Har yanzu dai bai amsa sakon da aka aike masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here