Wata bakuwar cuta ta bulla a Katsina

0
92

Akwai bukatar Gwamnatin Jihar Katsina ta gaggauta daukar mataki dangane da labarin bullar wata sabuwar cuta a kananan kukumomin batagarawa da Kurfi.

Bayan da wakilinmu ya samu daga na wani malamin asibiti da baya son a ambaci sunansa a Katsina, ya tabbatar da hakan inda ya kara da cewa abin ma ya hada har da karamar Hukumar Kurfi, bakuwar cutar ta bulla.

Wata cuta ce da take matukar damun duk wanda ya kamu da ita, inda aka ce tana sa ciwon kafa mai tsanani wanda cikin ‘yan kwanaki kadan sai ta cinye naman kafar.

Bugu da kari, mutanen da ke kamuwa basu da masaniyar abin da ke sa kamuwa da cutar, koda yake dai suna kiran cutar da sunan Daji.

Yana daga abin da ke kara samar da matsala ko taimakawa wajen karuwar yaduwar cutar rashin zuwa asibiti daga wadanda suka kamu da ita, sun gwammace su yi amfani da maganin gargajiya ko kuma su je Chemist su sayi magani.

Bayanai sun nuna mai yiwuwa ana daukar cutar ce ta hanyar amfani da gurbataccen ruwan sha, watakila saboda halin da ake ciki na rashin kudade a tsakanin Talakawa.
Masana sun bayyana akwai yiyuwar kwayar cutar ‘bacteria’ da take cin tsokar naman jikin dan’adam da ake kira da suna “Necrotizing fasciitis”, a cikin cutar.

Abubuwan da ake gani ko alamun an kamu da cutar sun hada da tsananin ciwo a gabar da cutar ta bulla, mutum yakan ji kamar tamkar an hada wata wuta a gabar, da kumburi daga nan kuma sai a kamu da zazzabi.

Sauran alamomin su ne akwai manyan kuraje da bakin tambari a wurin da cutar ta kama, sannu a hankali har kalar fatar jiki ta rika sauyawa ta fara zubar da ruwa mai wari.
Daganan sai mara lafiyar ya rika ganin jiwa, yawan gajiya, wani lokacin ma sai gudawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here