A wani labarin kuma, Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta nesanta kanta daga goyon bayan Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa da gamayyar kungiyoyin Arewa suka yi.
Mista Saidu, shugaban kungiyar Arewa mazauna Kudancin Najeriya, ya ce amincewa da Mista Akpabio a takarar shugabancin majalisar dattawa zai haifar da halaka ga Arewacin Najeriya.
Mamba a kungiyar ACF, Musa Saidu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Mista Saidu wanda kuma shi ne shugaban kungiyar Arewa mazauna Kudancin Nijeriya, ya ce amincewa da Mista Akpabio a matsayin shugabancin majalisar dattawa zai durkusar da Arewacin Nijeriya.
“Don haka muna nesanta kanmu daga amincewa da Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa da gamayyar kungiyoyin Arewa suka yi.
“Gamayyar kungiyoyin ba sun yi magana ba ne da yawun ‘yan Arewa, sun yi magana ne bisa radin kansu.
“Ba wata kungiyar Arewa ta gaskiya da za ta so amincewa da Akpabio a kan wani muhimmin matsayi irin na shugaban majalisar dattawa, saboda ba shi da alaka da Arewa.
“Mu ne mutanen da suka san Akpabio saboda mu mazauna Kudu ne, mun san wadanda ke son mutanen Arewa kuma Akpabio ba ya cikin su,” in ji shi.
Saidu ya kara da cewa tabbas gamayyar kungiyoyin sun amince da hakan ne bisa jahilci.
“Ina so in yi Allah wadai da amincewar da gamayyar kungiyoyin suka yi wa Akpabio, saboda sun yi hakan ne a kan jahilci.
“Zai iya yiyuwa an bai wa kungiyoyin cin hanci har tasa suka yi kwarin gwiwar amincewa da Akpabio.
“Ina tabbatar da cewa ‘yan Arewa ba mabarata ba ne da za su goyi bayan mutanen da ba su son su,” in ji shi.
Saidu ya ce ACF za ta ci gaba da yaki ko yin magana kan rashin adalci a kasar nan.
“Me ya sa jam’iyyar APC za ta himmatu wajen mayar da kujerar shugabancin majalisar dattawa ta 10 zuwa Kudu alhali muna da mutanen da suka cancanta a Arewa.
“Arewa maso yamma sun bai wa APC kuri’u mafi yawa a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, to me zai sa a hana su a dauka a bai wa wata shiyyar.
“Ina ganin lokaci ya yi da jam’iyyar za ta bai wa shiyyar ladan kuri’u masu yawa da ta bayar maimakon fara neman wani daga Kudu a matsayin shugaban majalisar dattawa,” in ji shi.
Gamayyar kungiyoyin Arewa sun amince da Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa, inda suka ce shi ya fi dacewa da wannan mukamin.
Baya ga Mista Akpabio, tsohon gwamnan Jihar Abiya, Orji Uzor Kalu da tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari duk sun bayyana sha’awarsu ta zama shugaban majalisar dattawa ta 10.