An kammala manyan gidajen yarin Kano da Abuja – Aregbesola

0
85

Wata sanarwa daga ma’aikatar cikin gida, ta ambato Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola na cewa  an kammala aikin gina sabbin gidajen yari na Kano da Abuja, kuma idan ana samar kuɗi a kai a kai, za a kammala sauran ma.

Dangane da ƙoƙarin rage cunkoso a gidajen yarin, Rauf Aregbesola ya ce daga shi har babban kwanturolan gidan jarin ƙasar, ba su da ikon sakin ɗaurarre.

Ya ce minista da babban kwanturola ba su da ikon tsarewa ko sakin kowa. Ana kai mutane gidajen yari ne da ingantacciyar takardar kotu, kuma ta wannan hanya ce kaɗai ake sakin ɗaurarru.

Haka kuma, in ji shi, shugaban ƙasa ko gwamna suna iya amfani da ikon da suke da shi na yin afuwa wajen sakin ɗaurarre.

Aregbesola ya ce: “Wani babban ƙalubale ɗaya da muke da shi a gidajen yari, shi ne cunkoso, musamman a cibiyoyin tsare mutane a birane inda ake da yawan jama’a, kuma harkokin al’umma ke da wuyar sha’ani, abin da ke janyo yawan aikata laifuka da buƙatar a tsare wasu mutane.

Ya ce suna ƙoƙari wajen shawo kan wannan ƙalubale ta hanyar gina manyan gidajen yari guda shida a dukkan shiyyoyi guda shida na Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here