Bankin musulunci zai ba wa Afirka $8bn domin noma da raya karkara

0
111

Bankin Raya Musulunci (IsDB) ya bayyana shirinsa na zuba jarin da ya kai Dala biliyan 7.8 a fannin noma da raya karkara a Afirka cikin shekaru biyar masu zuwa.

Shugaban bankin, Dokta Mohammad Al Jasser ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da Shugaban Bankin Raya Afirka AfDB), Akinwumi Adesina a yayin taron shekara-shekara na IsDB da ke gudana a birnin Jeddah na kasar Saudiyya.

A yayin ganawar, shugabannin biyu sun yi musayar ra’ayi kan hanyoyi da hanyoyin karfafa hadin gwiwa tare da magance kalubalen duniya.

Al Jasser, ya bayyana gamsuwa da hadin gwiwar IsDB da AfDB, tare da cewa, cibiyoyin biyu sun ba da gudummawar ayyukan da suka kai sama da Dala biliyan 8.3 a cikin kasashe mambobinsu 27.

Don haka, suke na duba yiwuwar kara kaimi a yankin musamman a  bangaren noma da raya karkara.

Hakan a cewarsa zai kawo cigaba mai dorewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here