Haƙƙin ciyar da ɗaurarru a gidajen yari ya koma kan gwamnoni’

0
55

Gwamnatin tarayya a Najeriya ta ce za ta daina ciyar da fursunonin jihohi da ke tsare a gidajen yarin ƙasar daga ƙarshen wannan shekara.

Ta shawarci jihohin ƙasar su yi cikakken amfani da gyaran fuskar da aka yi wa tsarin mulkin Najeriya a baya-bayan nan, don kyautata rayuwar fursunoninsu.

Wata sanarwa daga ma’aikatar cikin gida, ta ambato Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola na cewa matakin, zai fara aiki ne daga ranar 31 ga watan Disamban 2023.

Ya yi shelar cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan dokar yi wa tsarin mulkin Najeriya gyaran fuska, abin da ya cire harkar kula da gidajen yari daga ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya kaɗai, zuwa ƙarƙashin ikon haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da jihohi.

Don haka in ji sanarwar ma’aikatar cikin gida “Daga ranar 1 ga watan Janairun 2024, gwamnatin tarayya za ta daina ciyar da ɗaurarrun da suka aikata laifuka a jihohi amma ake tsare da su a gidajen yarin tarayya.

Jazaman ne kuma, jihohi su fara yin kasafin kuɗi don ciyar da ɗaurarrunsu da ke gidajen yarin tarayya a daidai lokacin da muke jiran su gina gidajen yari na kansu.”

Ya ce matakin zai taimaka wajen ƙara rage cunkoso a gidajen yarin Najeriya.

Ministan ya ce mutanen da suka aikata laifi a jihohi ne fiye da kashi 90% na ɗaurarrun da ke gidajen yarin Najeriya a yanzu.

Ministan cikin gidan ya nanata buƙatar yin cikakken gyaran fuska ga tsarin gudanar da shari’ar laifuka wanda ya ce zai taimaka wajen rage alƙaluma masu tayar da hankali na mutanen da ke jiran shari’a a gidajen yari.

Sanarwar ta ambato ministan na cewa abu ne mai muhimmanci, gwamnatocin jihohi su fara zuba kuɗi cikin harkar kula da gidajen yari.

Amma ministan ya ce, “Abu mafi muhimmanci shi ne buƙatar yi wa tsarin shari’ar laifuka garambawul.

Na sha yin wannan magana, kuma zan ci gaba da yin ta, cewa kashi 70 na mutanen da ake tsare da su a gidajen yari, suna zaman jiran shari’a ne”.

A cewar Rauf Aregbesola, wani abin takaici game da haka shi ne “bisa doka ba za mu iya fara ƙoƙarin gyaran halayensu ba, saboda ana ɗaukar su a matsayin marasa laifi, sai dai waɗanda bisa raɗin kansu suka zaɓi shiga”.

“Da yawansu sun shafe tsawon lokaci fiye ma da zaman hukunci na laifin da ake zargin sun aikata,” Aregbesola ya ce.

Hakan, in ji shi yana sanya su nuna halayyar neman tashin hankali kuma su ne babban ƙalubale ga sha’anin tabbatar da ɗa’a da ikon kula da cibiyoyin tsare mutane a Najeriya.

Ya ce kamata ya yi gwamnatocin jihohi, su yi garambawul ga tsarin gudanar da shari’o’insu, ta hanyar sanya iyaka a tsawon lokacin da ya kamata a kammala shari’a don tabbatar da yin shari’o’i cikin sauri.

Hakan a cewar ministan cikin gida, zai kawo ƙarshen dogon lokacin da ake kwashewa ana shari’a da kuma tsare mutane tsawon lokaci maras iyaka, a kan zargin aikata laifi da kuma rashin adalcin da ke tattare da haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here