Masu sace mutane suna garkuwa da su domin neman kudin fansa na ci gaba da cin karensu ba babbaka bayan samun saukin lamarin lokacin gudanar da zabukan 2023.
Abin ya zama ruwan dare game duniya ta yadda hatta sarakuna iyayen kasa abin bai bar su ba, inda ‘yan bindigar ke ci gaba da keta alfarmarsu tare da na sauran ‘yan kasa masu bin doka da ba-su-ji-ba-ba-su-gani ba.
A ci gaba da kai hare-haren masu garkuwar, a farkon makon nan sun afka fadar Mai Martaba Sarkin Kagarko, Alhaji Sa’ad Abubakar mai shekara 103 a duniya, da ke unguwar Rimi, a Karamar Hukumar Kagarko da ke Jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da wasu daga cikin iyalinsa har mutum takwas.
Bugu da kari, bayan ‘yan bindigar sun fice daga gidansa ne kuma a kan hanyarsu ta fita daga garin suka sake yin awon gaba da wasu mutum hudu.
LEADERSHIP Hausa ta yi tattaki na musamman har zuwa fadar Mai Martaba Sarkin na Kagarko domin gano takamaimen abin da ya faru.
Mai martaba Sarkin wanda ya tarbi wakilinmu da hannu biyu-biyu, ya wakilta Galadiman Kagarko, Alhaji Sa’adu Sulaiman wanda har ila yau shi ne shugaban ma’aikata a fadar sarkin mai daraja ta biyu, ya yi mana bayanin abin da ya faru dalla-dalla.
Sarkin na zaune, Galadiman ya fara da bayanin cewa, lamarin ya faru ne a ranar 7 ga watan Mayun shekarar 2023 da misalin karfe 10 da rabi na dare, masu garkuwa da mutanen suka je gidan sarki bayan an yi ruwa an dauke.
“Sun shiga har dakinsa, da farko sun yi kokarin shiga ta kofar dakin, to ba su samu iko ba, sai suka fasa tagar dakin ta hanyar balle karafan tagar da gatura da kuma wasu karafa, amma ba su yi harbi da bindiga ba, sun same shi (sarkin) a daki tare da wasu ‘ya’yansa da jikokinsa wadanda suke tare da shi a wannan daren.
“Sun samu mai martaba a kan gadonsa, to, a lokacin da suke kokarin shigowa dakin, daya daga cikin ‘ya’yansa da ke cikin dakin da ya leka ya ga abin da ke faruwa, sai ya sanar da shi, sai sarki ya ce masa ya buya.
“Mutum na farko da ya shigo daga cikin barayin sai ya zauna a dakin ya ce (wa sarkin) ya bashi kudi, mai martaba ya nuna musu cewa ba shi da kudi. Ya ce da sarki kowane irin kudi ne in yana da shi ko Dalar Amurka ce ya bashi. Sarki ya ce to wa ya ce maka ina da kudi? Wanda ya ce maka ina da kudi ya zo ya dauka ya ba ka amma ni ba ni da kudi,” in ji mai magana da yawun sarkin.
Galadiman ya ci gaba da cewa, “dan bindigar ya ce wa sarki baba ba ka ga muna da bindiga ba? sarki ya ce bindiga ni ba ta ba ni tsoro, na san abin kashe mutane ce amma ni ba ta ba ni tsoro, don haka ni ba ni da kudi.
“Daga nan ne suka kyale sarkin, amma sauran ‘ya’ya da jokokin da suka samu suna kwance suna bacci a dakin duk sai suka tattara su suka tafi da su.”
Har ila yau, Galadiman na Kagarko ya bayyana yadda al’amarin ya shafi bangaren matan mai martaba sarkin, yana mai cewa, “akwai matarsa guda daya da suka dauka sunanta Maryam, ita Maryam lokacin da wadannan bata-gari suka shigo ta ji fasa gilashin tagarsa da saran wadannan makaran da aka sanya, to sai ta hasko cocilan, ganin wannan cocilan ta tagarta, sai suka tasamma dakinta inda nan ma suka fasa, kofar ba ta shigu ba, ta taga ita ma suka fasa suka karya karafan sannan suka sakala hannunsu suka bude kofar, suka shiga suka same ta da ‘ya’yanta guda biyu suna kwance, inda suka kwashi yaran matan guda biyu.
“Ita matar sun dauke ta, lallai har sun fita da ita gidan, sun fara tafiya da ita to ba ta iya tafiya irin yadda suke so, to ganin ta gajiya sai suka sako ta ta dawo gida”, in ji shi.
Da aka tambaye shi ko wadannan masu garkuwa sun kira waya domin bayyana dalilinsu na aikata hakan ko kuma bukatarsu ta karbar kudin fansa? Ya ce, “kamar yadda ka sani yaran da suka kwashe ma wasu ba su da waya a hannunsu, sun dai kwashi wayar wasu a gidan wadanda suka ji tsoro suka gudu sun ga wayoyin mutane sun kwashe, amma dai kamar dai yadda na gaya maka takamaimai har yanzu babu wata magana da aka yi da su, kuma sun shafe tsawon lokaci suna abin da suka ga dama ba tare da martani daga jami’an tsaro ba.”
“Haka nan, mu dai abin da muke ganin ya faru ko kuma shi ne musabbabin wannan, a kwanakin baya kamar kwana biyar da suka wuce (lokacin daukar rahoton), akwai jami’an sojoji da aka turo nan Kagarko, kuma saboda rade-radin da ake yi ne na wadannan mutane bata-gari suna dajin Janjala.
“Daga gwamnatin tarayya zuwa gwamnatin jiha an tura jami’an tsaro masu yawa da motocinsu da abincinsu da makamansu sun shiga wannan daji kuma sun samu nasarar kama wadansu masu ba wa masu garkuwar bayanan sirri. To a sakamakon haka ne muke ganin ba su ji dadin abin da aka yi wa jama’rsu ba, shi ne suka ga ya kamata su fara da gidan mai martaba domin nuna ishara ga jama’a, tunaninmu dai abin da ya faru kenan,” in ji shi.
An tambaye shi ko gwamnatin Jihar Kaduna ta yi magana da su game da faruwar wannan lamari zuwa lokacin tattaunawarsa da wakilinmu, Galadiman ya ce, zuwa yanzu dai ba su riga sun samu sakon gwamnati ko daya ba, tun da abin ya faru a daren Litinin wato ranar Lahadi, amma duka mun aika wa da gwamnati sakonni na abubuwan da suka faru.
“Shi Kwamishin Tsaro da Harkokin cikin Gida, mun rubuta masa wasika, mun kuma aika wa kwamishinan ‘yansanda, mun kuma aika wa dukkan jami’an tsaro na wannan karamar hukuma, wanda yake wakilan gwamnati ne su ma duk mun sanar da su, kuma wasunsu sun ziyarci mai martaba sun ji daga bakinshi sun gane ma idonsu abin da ya faru a gidansa”.
Ganin irin yadda aka keta tsakiyar garin na Kagarko aka tafka wannan ta’asa, ko akwai wani mataki da masarautar ta dauka domin riga-kafi, Galadiman ya ce matakin dai ba zai wuce sanar da gwamnati da jami’an tsaro ba.
“Mun sanar da gwamnati kuma muna kan daukar matakai bakin gwargwado yadda za mu iya, sannan kuma da yin addu’o’i na neman kariya daga ubangiji Allah Subhanahu Wata’alah,” in ji shi.
Wakazalika, wata majiyar ta shaida mana cewa, an ga wani a cikin masu garkuwa da mutanen sanye da hula hana-Sallah a kansa da yake nuna musu hanya a gidan, wanda hakan ya alamta cewa lallai shi ne dan leken sirin da ya jagorance su shiga gidan musamman yadda ya yi saurin bacewa bayan an yi garkuwa da mutanen da diba.
Har ila yau, LEADERSHIP Hausa ta ji ta bakin Sakataren Masarautar Kagarko, Malam Yahaya Ibrahim, kan abin da ya faru, inda ya yi kira ga gwamnati a dukkan mataki da ta dubi Allah ta taimaka wajen ganin an kubutar da wadannan bayin Allah da masu garkuwa suka kama ba tare da sun cutar da su ba.
Sannan ya nemi hukuma ta taimaka musu da jami’an tsaro domin ganin masarautar ta barranta daga wadannan hare-hare, yana mai cewa, “Mun rubuta takarda zuwa kwamishinan tsaron cikin gida, mun rubuta wa kwamishinan ‘yansanda don a turo mana jami’an tsaro domin su kare gidan mai martaba da yankin Kagarko gaba daya, mun rubuta wa sojoji da Sibil Difens da ‘yan banga duka mun rubuta musu.”
Sai dai kuma, masarautar ta koka kan nuna halin ko-in-kula da shugaban karamar Hukumar Kagarko ya nuna kan faruwar lamarin inda ta ce tun da lamarin ya faru bai zo domin jajanta musu shi da kansa ko aiko da wasu wakilai ba.
A cewar masarautar wani kansila ne guda daya ya zo shi ma don kansa.
Wata majiya da nemi a sakaya sunanta daga garin na Kagarko, ta yi wa LEADERSHIP Hausa karin bayanin cewa, dole ne jama’a su zama cikin shiri ganin yadda aka fara abin daga fadar sarki.
Majiyar ta ce, a halin yanzu dai mutane na cikin halin dar-dar a garin.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto dai ba mu samu wani bayani daga masarautar dangane bukatar da maharan suka gabatar wa masarautar ba ko kuma wata sanarwa a hukumance daga gwamatin jihar Kaduna ko rundunar ‘yansanda.
A makon da ya gabata ne dai jami’an sojoji suka yi awon gaba da wasu mutane daga cikin garin na Kagarko da kauyen Janjala su 10 da kuma Madakin Janjala bisa zargin suna da hannu a kan ta’addancin ‘yan bindiga a yankin, inda ake ci gaba da bincike.