Za mu dauki sabbin matakan tunkarar makaman nukiliya – Rasha

0
104

Rasha ta ce matakin da Birtaniya ta dauka na kai makamai masu linzami masu cin dogon zango na Storm Shadow zuwa Ukraine wani mataki ne na tsokana.

Ta hanyar sanar da cewa za ta isar da makamin da aka harba ta iska, Biritaniya ta zama kasa ta farko da ta samar da makamai masu cin dogon zango zuwa Kyiv.

Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta ce “Muna kallon wannan matakin a matsayin wani yunkuri na nuna kyama daga birnin Landan, da nufin mika makamai zuwa Ukraine domin kara dagula lamura.”

Makamin mai linzami wanda za a iya sarrafa shi cikin matsanancin yanayi, sojojin Birtaniya da na Faransa sun taba amfani da shi a yankin Gulf, Iraki da Libya.

“A bayyane yake Birtaniyya ta tsallake duk wata iyaka domin daukar wannan rikici zuwa wani sabon mataki na barna da asarar rayuka,” in ji Moscow.

Rasha ta ce za ta dauki dukkan matakan da suka dace don kawar da barazanar da sabbin makamai masu linzami za su yiwa kasarta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here