An sake tono gawarwaki 29 na wadanda suka mutu da yunwa don kwadayin shiga Aljanna

0
104

Hukumomi a kasar Kenya sun tono gawarwaki mafi yawa a rana guda daga wani wuri da aka binne mutanen da suka yi azumin mutuwa.

‘Yan sanda sun tono gawarwaki 29, ciki har da yara 12 daga dajin Shakahola da ke yankin Kilifi na kasar Kenya.

Akalla mutum 179 wadanda mambobin cocin Good News International Church ne aka tabbatar da sun rasu.

Hukumomi a kasar sun tabbatar da cewa adadin jama’ar da ba a gani ba wadanda mambobin cocin ne sun kai 600, kamar yadda kungiyar agaji ta Red Cross reshen Kenya ta bayyana.

Tuni ‘yan sanda suka kama shugaban cocin Paul Mackenzie da matarsa. An bayyana cewa ya bayar da umarni ga mabiyansa da su zauna da yunwa har su mutu domin su samu rabon shiga aljanna.

Jaridun kasar sun ruwaito ‘yan sanda suna cewa za a ci gaba da bincike ta harabar gidan faston inda ake zargi a nan ma an binne gawarwaki da dama.

Likitan gwamnati wanda ke bincike kan gawarwaki ya ce akasari sakamakon bincike kan gawarwakin ya nuna cewa sun mutu ne sakamakon yunwa ko kuma shake su ko kuma kashe su da duka.

An ci gaba da kashi na biyu na aikin tono gawarwakin a wannan makon bayan an dakatar da aikin saboda rashin yanayi mai kyau.

Hukumomi a Kenya sun fito fili sun bayyana gazawarsu ta bangaren kare jama’ar da suka rasu kuma Shugaba William Ruto ya kafa wani kwamitin bincike wanda za yi bincike kan matsalolin da aka samu da suka yi sanadin mutuwar mutanen.

Haka kuma kwamitin zai yi aiki wurin sake bitar ayyukan kungiyoyin addini a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here