Hukumar Alhazai ta amince da ƙarin dala 250 kan kujerar aikin hajji

0
101

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta amince da ƙarin dala 250 a kan kowacce kujerar aikin hajjn bana, kamar yadda kamfanonin jiragen aman da za su yi jigilar alhazan suka nema.

Shugaban hukumar Alhzan ƙasar Zikrullah Hassan ne ya tabbatar da haka a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki na hukumar a Abuja babban birnin ƙasar.

Ya ce ”Bayan tattaunawa mai zurfi tare da kamfanonin da za su yi jigilar maniyyatan mun amince da ƙarin dala 250 a kan kowacce kujerar aikin hajji ta wannan shekara”.

Kwamishinan kuɗi da ma’aikata na hukumar Nura Hassan Yakasai, ya shaida wa BBC cewa kamfanonin jigilar alhazan ne suka buƙaci hakan saboda yaƙin da ake a Sudan, ya sanya dole sai sun zagaya, ba za su bi ta sararin samaniyar Sudan ba.

Ya ce kamfanonin jiragen sun ce sai sun yi zagaye na ƙarin sa’o’i biyu, kuma a kowacce sa’a kamfanonin sun ce jiragen kan sha mai na kusan miliyan takwas.

A don haka ne hukumar da kamfanonin jiragen suka amince da ƙarin dala 250 a kan kowacce kujera.

Haka kuma ya tabbatar da ƙarin kuɗin biza da aka yi na wajen dala 65.

To sai dai ya ce hukumar na tattaunawa da gwamnati domin ganin yadda za a biya ƙarin ƙuɗaɗen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here