Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta aminta da kudurin dokar kayyade tsada da almubazzaranci a bukukuwan aure, zanen suna, kaciya da makamantan su a jihar.
Honarabul Faruku Mustapha Balle (PDP- Gudu) da gudunmuwar Abubakar Shehu Shamaki (APC- Yabo) ne suka gabatar da dokar waddd Majalisar ta aminta da ita a matsayin doka a zaman ta na wannan makon.
Tun da farko, bayan tsallake karatu na biyu, Majalisar ta gabatar da kudurin dokar a gaban kwamitin ta na sha’anin Addini wanda ya gabatar da rahotonsa a ranar Talata tare da samun amincewar manbobin majalisar da kudurin a matsayin doka.
Da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin, Abubakar Shamak ya bayyana cewar sun tattauna da masu ruwa da tsaki a Sakkwato wadanda suka bayar da gudunmuwar da aka yi amfani da ita a cikin dokar wadda za ta amfani al’umma.
Bayan muhawara, kudurin ya samu amincewar zama doka a zaman majalisar da Mataimakin Shugaban Majalisar, Honarabul Abubakar Magaji ya jagoran ta.
Honarabul Shamaki ya bayyana cewar dokar na da manufar kayyade da takaitawa daidai gwargwado kan tsada da sharholiya da ake yi a bukukuwan aure, zanen suna da kaciya a Sakkwato.
Ya ce ko shakka babu dabi’ar almubazzaranci da ake yi da sunan bukukuwa ba karamar illa ba ce wadda ke haifar da tabarbarewar tattalin arziki a cikin al’umma.
“Wannan bakar dabi’ar idan aka ci-gaba a haka ba tare da daukar mataki da kayyadewa ba, za ta sa aure ya yi wa jama’a matukar wahala wanda hakan zai iya haifar da zina, madugo, luwadi da sauran ayyukan assha.
Dan Majalisar ya kara da cewar a yanzu haka kasawar ango ga yin hidimar da aka bukata ta sharholiya a yayin aure na haifar da watsewar auren bakidaya.
“Matsalar ta haifar da yawaitar mace- macen aure a cikin al’umma. Don haka wannan dokar za ta taimaka kwarai wajen rage tsadar aure da sharholiyar da ake yi da takaita yawan zawarawa.” Ya bayyana.