Me ya sa shugabannin ƙasa ke son yi wa Majalisar Najeriya tuwona-maina?

0
83

Kimanin mako biyu a rantsar da sabuwar gwamnatin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a Najeriya, amma ƙura na ci gaba da turnuƙewa a fagen siyasar ƙasar game da shugabanci majalisa ta goma.

Jam’iyya mai mulki wato APC ta ce tana nan kan matsayinta na goyon bayan Sanata Godswill Akpabio da Sanata Barau Jibrin a matsayin shugaban Majalisar Dattijai da mataimakinsa, da kuma Tajuddeen Abbas da Benjamin Kalu a matsayin shugaban Majalisar Wakilai da mataimakinsa.

Sauran masu neman shugabancin a majalisun biyu, sun yi tattaki har shalkwatar APC a Abuja, inda suka gabatar da rashin yardarsu a kan matakin uwar jam’iyyar tasu.

A ranar Juma’a ma, mataimakin shugaban Majalisar Wakilai mai ci, Ahmed Idris Wase ya ƙaddamar da takarar neman shugabancin sabuwar majalisar da za a buɗe nan gaba a watan gobe.

APC dai ta ce ta raba muƙaman ne don tabbatar da adalci da tsarin raba daidai a tsakanin shiyyoyi guda shida na Najeriya, sai dai masu adawa da matakin sun ce yin haka, rashin adalci ne tun da majalisa gashin kanta take ci, kuma jama’a take wakilta, ba jam’iyya ko wani shugaba ba.

Yayin da wasu ke kallon lamarin da cewa yunƙuri ne na shiga aikin majalisar, don ganin ta zama ‘yar amshin shata ga ɓangaren zartawa.

BBC da haɗin gwiwar Gidauniyar McArthur a baya-bayan nan ta gayyaci wasu masu ruwa da tsaki wani taro don tattaunawa a kan ko me ya sa shugabannin ƙasa a Najeriya ke son tabbatar da shugabancin majalisa?

Katsalandan

Wani babban ƙalubale da majalisun dokoki ke fama da shi a Najeriya in ji wani masanin kimiyyar siyasa, Mallam Kabiru Sufi, shi ne katsalandan.

A cewarsa, ko kasafin kuɗi ɓangaren zartarwa ya kai don a zartar da shi zuwa doka, to ba a sakarwa majalisa mara ta yi abin da ya dace.

Ya ce lokaci zuwa lokaci, ɓangaren zartarwa yana ƙoƙarin ganin ya shiga cikin aikinsu, ko kuma ya tursasa musu, su yi wani abu da bai kamata ba.

Mallam Sufi ya ce hakan kuma yana kawo tarnaƙi a ayyukan majalisa, ta yadda matakin ke zagon ƙasa ga tsarin rabon iko daidai tsakanin ɓangarorin gwamnati uku.

Shi ma, zaɓaɓɓen sanata kuma tsohon ɗan majalisar wakilai, Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce matuƙar ‘yan majalisa za su yi aikinsu na yin doka da bibiyar ayyuka yadda ya kamata, to ɓangaren zartarwa ba zai miƙe ƙafa yadda yake so ba.

Ya yi zargin cewa ɓangaren zartarwa musamman a ƙasashe masu tasowa na son ganin ya yi ‘cinye duk’ wato ya tattare ikon komai a ƙarƙashinsa.

Shi kuwa wani ɗan fafutuka daga ƙungiyar wayar da kai kan ayyukan ‘yan majalisa (CISLAC) Auwal Musa Rafsanjani, cewa ya yi abu ne mai muhimmanci a samu haɗin kai tsakanin majalisar dokoki da ɓangaren zartarwa.

Amma ba haɗin kan da zai hana majalisa ta yi aikinta na kare tsarin mulki da muradan al’ummar ƙasa ba, in ji shi.

A cewarsa, lamarin zai fi muni, idan majalisa ta kasa aikinta a lokacin da ake ganin ɓangaren zartarwa yana wuce gona da iri.

Kawu Sumaila dai ya yi iƙirarin cewa, akwai rashin dacewa a ce “wani mutum a ɓangaren zartarwa ne zai naɗa shugabanni a majalisun da ke wakiltar muradan ‘yan ƙasa”.

“Sunansu Majalisun ƙasa, masu wakilcin jama’ar da suka zaɓo su don kare muradansu,” in ji zaɓaɓɓen sanatan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here