Tasirin gwamnoni a zaben majalisar dokokin Najeriya

0
105

Wasu mutane da yawa a ƙasar na ra’ayin cewa gagarumin ikon da gwamnoni ke da shi a harkokin mulki da na siyasa, na cikin ƙalubalen dimokraɗiyya a Najeriya.

Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce maganar gwamnoni da cewa jagoranci na jam’iyya a hannunsu yake, babban tarnaƙi ne dimokraɗiyyar ƙasar.

“Matuƙar gwamna ne zai naɗa shugaban ƙasa. Shi zai naɗa shugaban majalisar dattijai. Shi zai ba da mataimakin shugaban ƙasa. Da shugabannin jam’iyya. Ya naɗa kansila. Ya naɗa ɗan majalisar tarayya da kowa da kowa. Sai abin da yake so, to ba mutane za a wakilta ba, gwamna za a wakilta”, in ji shi.

Ghali Umar Na’abba ya ce ‘yan majalisa da yawa ba su cancanta ba, don haka idan sun zo majalisa, aikin gwamna suke yi ba na jama’a ba. “Duk abin da gwamna ba ya so, ba za ka ga ana tattauna shi a majalisa ba”.

Auwal Musa Rafsanjani ya ce akwai buƙatar yi wa tsarin mulkin Najeriya garambawul don rage ɗumbin ikon gwamnoni, matuƙar ana so abubuwa su ci gaba ta fuskar mulkin dimokraɗiyya ƙasar.

Ikon gwamnoni a Najeriya ya yi yawa. A cewarsa: “Hatta shugaban ƙasa, tsoronsu yake ji. Su ne za su kawo masa ministoci, su ne za su kawo masa mutanen da zai naɗa shugabannin hukumomi da jakadu.

Kawu Sumaila ya ce dole ne tun daga matakin zaɓe, a riƙa ɗauko ‘yan majalisar da za su yi al’umma alƙawari maimakon tsarin da ake kai wanda gwamna yake nuna mutanen da za su kasance ‘yan majalisa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here