Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya ce a kama dan gidan Fela

0
103

Babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya Usman Alkali Baba ya bayar da umarnin kama mawakin kasar Seun Kuti, wanda ake zargi da dukan wani dan sanda.

A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga wani da ake zargin mawakin ne yana cin zarafin dan sandan.

A sanarwar da rundunar ‘yan sandan kasar ta fitar, babban sufeton ‘yan sandan ya ce kwamishinan ‘yan sandan Jihar Legas ya gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Sai dai a martanin da mawakin ya mayar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce dan sandan ya yi niyyar kashe shi ne da iyalinsa, sa’annan kuma ya ce yana da shaida kan hakan.

Mawakin kuma ya ce yana maraba da binciken da za a yi a kansa kuma zai bayar da cikakkiyar gudunmawa.

Sa’annan ya bukaci babban sufeton ‘yan sandan da ya hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Seun Kuti shi ne dan autan marigayi Fela Kuti, fitaccen mawakin nan na Nijeriya wanda ya yi suna a shekarun 1970 da 1980.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here