Home Labarai Wasanni Barcelona ta lashe kofin La Liga karon farko tun shekarar 2019

Barcelona ta lashe kofin La Liga karon farko tun shekarar 2019

0
117

Yayin wasan na jiya dai Lewandowski ya fara zura kwallo a minti na 11 kana Balde a minti na 20 yayinda Lewandowski ya kara ta 3 a minti na 40 wanda ke nuna tun gabanin tafiya hutun rabin lokaci Barcelona ke jagoranci da kwallaye 3 da nema.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne kuma Kounde ya karawa Barcelona kwallonta na 4 ko da ya ke Espanyol ta farke kwallaye 2 ta hannun Puado da Joselu.

Barcelonar dai ta yi nasarar ne da gagarumar tazara tsakaninta da babbar abokiyar dabinta wato Real Madrid wadda suka tisa tseren lashe kofin tare, domin kuwa maki 14 ke tsakaninsu.

Sai dai duk da nasarar ta Xavi bayan gagarumin koma bayan da Barcelonar ta samu a duniyar kwallo, manajan mai shekaru 43 na da gagarumin aiki a gabansa ganin yadda kungiyar ta Catalonia ta gaza taka rawar gani a tsakanin takwarorinta kungiyoyin Turai, wato walau a gasar zakarun Turai ko kuma kanwarta Europa.

An ga dai yadda Barcelonar ta yi waje daga gasar cin kofin zakarun Turai tun a matakin rukuni yayinda ko a Europa dinma ba a barta ba inda Manchester United ta yi waje da ita.

Manajan dai na ci gaba da shan suka, lura da yadda aka tsammaci zuwansa Club din a shekarar 2021 ya taka rawa kwatankwacin Pep Guardiola a kakar wasa ta 2008.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

X whatsapp