Rigimar bashi: Yadda ma’aikatan banki suka kashe matar kwastomansu a jihar Ogun

0
87

Matar mai suna Vivian Omo, wanda ake zargin daya daga cikin ma’aikatan bankin ne mai suna Ajibulu, wanda shi ne yafi kaurin suna wajen sanadin mutuwar Matar bayan ya ture ta, sauran hudun: Badmus Olalekan, Ajibade Oludare, Eniola Aduragbemi da Femi Oloko an rahoto jami’an ‘yansanda sun cafke su baki daya a garin Ifo na jihar Ogun, inda lamarin ya faru.

LEADERSHIP ta tattaro cewa, ma’aikatan bankin da ke da ofishi a garin Ifo a karamar hukumar Ifo ta jihar Ogun, sun dira gidan kwastoman na su domin nemansa da ya biya bashin da ya karba, amma Matar ta shaida musu cewa Mijinta baya gida.

Amsar da Matar ta ba su sam ba ta yi wa ma’aikatan bankin dadi ba inda nan take suka fara tattara dukkanin kayayyakin alatu da ke gidan zuwa ofishinsu, amma marigayiyar ta hana su kwashe mata kaya.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), Abimbola Oyeyemi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce a lokacin da marigayiyar ke takaddama da ma’aikatan bankin, sai daya daga cikinsu mai suna Ajibulu ya tureta ta ke ta fadi a Sume aka garzaya da ita asibitin da ke kusa don ceto rayuwarta.

Amma Likitan da ke bakin aiki ya bayyana cewa “ta mutu”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here