Dorinar ruwa ta kifar da jirgi a Malawi

0
114

Akalla mutum 20 ne suka ɓace a Malawi bayan wata dorinar ruwa ta kifar da kwale-kwalen da suke ciki.

Hukumomi sun ce kwale-kalen na dauke da kusan mutum 37.

An gano gawar wani yaro wanda ɗaya ne daga cikin fasinjojin.

Ana nan ana gudanar da aikin ceto a kogin mai cike da kada da kuma dorinar ruwa, sannan kwale-kwalen mara inji ake amfani da su a kogin.

Dorinar ruwa na daga cikin dabbobi masu haɗari a Afirka , kuma kiyasi ya nuna suna kashe kusan mutum dari biyar a ko wace shekara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here