Gwamnatin Kaduna za ta taimaka wa matar da RFI ta yi hira da ita

0
101

Gwamnatin Jihar Kaduna da ke Najeriya ta sanar da kudirinta na taimaka wa wata mata da mijinta ke hana ta abinci,abin da ya sa take balaguro daga Jigawa zuwa Kaduna domin bara, yayin da mijinta ke can gida kwance yana jiran matar ta ciyar da shi duk da cewa, yana cikin koshin lafiya.

A yayin wata hira kai-tsaye a shafin Facebook na RFI Hausa, Kwamishiniyar Kula da Jin dadi da Walwalar Al’ummar Jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba, ta ce za su bai wa matar da ‘ya’yanta matsuguni, sannan kuma za su nemo mijinta don ladabtar da shi.

Kwamishiniyar ta ce, za su tuntubi hukumomin jihar Jigawa domin nemo wannan mutumin da ake ganin tamkar ya ci zarafin iyalinsa.

Matar wadda muka wallafa bidiyonta makwanni biyu da suka gabata ta bayyana irin bakar wahalar da take sha wajen ciyar da kananan yaranta hudu bayan mijin nata ya sake mata ragamar komai da komai.

RFI Hausa ta tarar da matar ce da yaranta zaune a karkashin wata bishiya a cikin birnin Kaduna suna cin kwadon garin kwaki cikin wani yanayi na tausayi.

Kazalika ba su da wurin kwana na kirki, yayin da suke gwamutsuwa a wani wuri da ke unguwar Hayyi Rigasa.

Gwamnatin Kaduna ta koka kan yadda irin wannan matsalar ta rashin kula da iyali ta zamo ruwan dare a arewacin Najeriya, inda wasu magidanta ke sakar wa matansu ragamar ciyar da iyali babu-gaira-babu-dalili.

Kofa a bude take ga duk wanda ke son tallafa wa wannan mata, kuma ana iya tuntubar Ofishin Kwamishiniyar Kula da Jin dadi da Walwalar Jama’ar Jihar ta Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here