Kotun Majistare ta ba da belin Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi

0
118

Kotun Majistare a Bauchi ta bayar da belin fitaccen malamin Musuluncin nan na jihar, Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi.

A ranar Talata ne kotun majistare ta 1 ta yanke hukunci a kan buƙatar beli da lauyoyin fitaccen malamin mai janyo ka-ce-na-ce, suka nema bayan an gurfanar da shi a gaban kotu.

A ranar Litinin ne, ‘yan sanda suka shigar da Sheikh Idris Dutsen Tanshi gaban babbar kotun majistare ta ɗaya, inda suka tuhume shi da tada hankulan jama’a.

Sai dai malamin ya musanta zargin.

Lauyoyinsa sun shaida wa kotu cewa laifin da ake zargin malamin da aikatawa ba zai hana a bayar da shi beli ba, bisa tanadin dokokin Najeriya.

Daga nan sai alƙalin kotu ya sanya Talata a matsayin ranar da zai yanke hukunci game da buƙatarsu. Sannan ya ba da umarnin a ci gaba da tsare malamin a gidan yari kafin zaman kotu na gaba a washe gari.

Wata ƙungiyar addini mai suna Fityanul Islam ce ta kai ƙorafi kan malamin, tana zargin sa da furta miyagun kalamai a kan Annabi Muhammadu, sai dai Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi da magoya bayansa sun ce zargin ba gaskiya ba ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here