Waɗanne ne sharuɗɗan da a ka sa na belin sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi?

0
109

Barista Alƙassim Muhammad, ɗaya daga cikin lauyoyin Sheikh Idris Abdul’aziz ya shaida wa BBC cewa kotun ta bayar da belin malamin ne bisa wasu sharuɗɗa.

Lauyan ya ambato kotu na cewa har yanzu dokokin Najeriya suna kallon malamin a matsayin wanda bai aikata wani laifi ba, don haka ba za a kama shi da laifi ba, har sai lokacin da aka tabbatar da da’awar da ake yi a kansa.

Ya ce sharaɗi na farko sai malamin ya gabatar da wani babban ma’aikacin gwamnati da ya kai matakin babban sakatare da kuma mai unguwa ko hakimi don su tsaya masa.

“Akwai kuma sharaɗin da za su gabatar da takarda, mallakan wani abu ko fili ko gida da ya kai naira miliyan biyar,” in ji Barista Alƙassim.

A cewarsa, kotu ta kuma buƙaci sai mutanen da za su tsaya wa Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi, su gabatar da hotunansu ga rijistaran kotu, kafin sakin malamin.

Tun da farko, rahotanni sun ce magoya bayan malamin sun cika harabar kotun ta Mai shari’a Abdulfatah Shekoni duk da ɗumbin jami’an tsaro da aka jibge waɗanda suka riƙa taƙaita shigi da ficen cincirindon mutane.

Barista Alƙassim Muhammad sai an cika dukkan sharuɗɗan belin ne kafin a saki Sheikh Idris Abdul’aziz.

Za a ci gaba da sauraron ƙarar

Mai shari’a Abdulfatah Shekoni dai ya sanya ranar Laraba 24 ga watan Mayu, don ci gaba da zaman sauraron shari’ar ta Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi da kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi.

Shari’ar dai ta ja hankalin ɗumbin mutane a ciki da wajen jihar.

A farkon watan Afrilu ne fitaccen malamin na jihar Bauchi ya furta wasu kalamai da suka tayar da ƙura a tsakanin takwarorinsa malamai da mabiyansu.

Yanzu dai za a zuba ido a gani shaidun da ɓangarorin biyu za su gabatar a wannan ƙara, kafin kotu ta kai ga yanke hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here