EFCC ta fara bincikar Shugaba Buhari da mukarrabansa – Matawalle

0
104

Gwamnan jihar Zamfara mai barin gado, Bello Matawalle ya bukaci hukumar EFCC mai yaki da cin hanci a Najeriya, da ta fara bincikar shugaba Buhari da manyan jamiā€™ansa da kuma ministoci, maimakon mayar da hankali kan gwamnonin da ke barin gado.

Manyan mukarabban shugaban kasar dai, sun kunshi mataimakin shugaban, da kuma mataimakan fadar shugabancin kasar da aka nada.

Matawalle ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar inda ya nuna shakku kan dalilin da ya sa EFCC ke binciken gwamnoni masu barin gado.

ā€œIna bukatar shugaban hukumar EFCC ya yi irin wannan gayyata ga jamiā€™an fadar shugaban kasa da mambobin majalisar zartarwa ta tarayya, wadda ita ce mafi girman matakin gwamnati a kasar nan,ā€ in ji shi.

Bello Matawalle zai sauka daga mukamin gwamna a ranar 29 ga watan Mayu bayan ya sha kaye a zaben da ya nemi waā€™adi na biyu.

Gwamnonin Najeriya sun fake da kariyar da kundin tsarin mulkin kasar ya basu, na kaucewa fuskantar tuhuma daga EFCC, inda a yanzu haka za su fuskanci hukumar da zarar sun sauka, cikin su kuwa har da gwamna Matawalle mai baring ado.

Sanarwar gwamnan na Zamfara, ta kuma zargi shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, da aikata rashawa, yana mai cewa yana da kwararan shaidu a kansa.

ā€œAkwai Ā bukatar ya bayyana mana, yadda ake sayar da kadarorin da EFCC ta kwace ba tare da bin kaā€™ida ba,ā€ inji Matawalle.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here