James Milner da Roberto Firmino da Naby Keita da kuma Alex Oxlade-Chamberlain za su bar Liverpool a karshen kakar nan, in ji kungiyar.
Kwantiragin ‘yan wasan hudu zai kare a kungiyar Anfield a karshen kakar nan.
Dukkansu suna cikin ‘yan wasan da suka lashe wa Liverpool Champions League a 2019 da kuma Premier League a 2019-20.
‘Yan wasan za a yi musu jinjinar ban girma ranar Asabar a karawar da Liverpool za ta yi a gida da Aston Villa a Premier League.
Tuni kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya fayyace yadda kungiyar ke bukatar shiga kasuwa, domin sayo karin ‘yan kwallo.
Milner da Firmino sun koma Liverpool a 2015 karkashin Brendan Rodgers, wadanda suka lashe Premier League a 2019 – da FA Cup a bara.
Tsohon dan kwallon Manchester City, Milner, wanda ya yi wa Liverpool karawa 330, ana akalanta shi da zai koma Brighton ko kuma Leeds.
Firmino shine dan wasan Brazil da ya ci kwallaye da yawa a tarihin Premier League tun a 2019, wanda yanzu ya ci 80 a fafatawa 254.
Za a tuna dan kwallon mai shekara 31 kan rawar da ya taka a cin kwallaye tare da Mohamed Salah da Sadio Mane a kungiyar Anfield.
Keita, wanda ya ci kwallo 11 a fafatawa 129 ya koma kungiyar a 2017, amma karawa 12 ya yi a kakar nan, wanda ke fama da jinya.
Shima Oxlade-Chamberlain mai fama da rauni ya buga wa Liverpool fafatawa 13 a bana – na karshe shine da Real Madrid a Champions League zagaye na biyu.
Mai shekara 29 ya je Anfield a 2017, wanda ya buga wasa 146 da cin kwallo 18.