Najeriya na bukatar Dala biliyan 12 don tsaftace Bayelsa

0
88
Wani sabon rahoto ya bayyana cewa, Najeriya na bukatar akalla Dala biliyan 12 domin gudanar da aikin tsaftace malalar man fetur a jihar Bayelsa da ke yankin kudu maso kudancin kasar.

Rahoton ya bayyana manyan kamfanonin man nan guda biyu wato Shell da Eni a matsayin wadanda suka gurbata jihar ta Bayelsa, kuma za a dauki sama da shekaru 12 ana aikin tsaftace jihar.

Ma’aikatar Mai da Muhalli ta jihar Bayelsa ce ta tattara bayanai bayan da a shekarar 2019, ta fara gudanar da bincike kan tasirin malalar man fetur a jihar.

Ma’aikatar ta kuma nazarci wasu hujjoji da ta samu tare da gudanar da gwaje-gwajen jini kan mutanen da ke rayuwa a yankunan da malalar man ta yi wa illa, inda ta gano cewa, akwai guba mai yawa da tsiyayar man ta yada a iska da ruwan sha har ma a cikin jinin al’umma.

Ma’aikatar ta ce, akwai sakacin kamfanonin wajen samun wannan  matsalar domin kuwa, sun gaza daukar matakan da suka dace na kariya.

An dauki shekaru masu yawa ana fama da wannan matsalar a jihohin da ke da arzikin man fetur a Najeriya da suka hda da Niger Delta da Rivers da Delta da Akwa Ibom da Bayelsa, lamarin da ya lalata gonaki tare da kashe halittun da ke rayuwa a cikin ruwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here