Yau 17 ga watan Mayu, 2023 ne ranar da Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta sanya domin komawa amfani da gajerun lambobin sanya kati da data na bai-daya a Najeriya.
Umarnin hakan da ke kunshe a cikin sanarwar da hukumar NCC ta fitar a watan Maris ya nuna daga yanzu, babu bambanci a gajerun lambobin sanya kati ko data dangoginsu a layukan duk kamfanonin sadarwa a Najeriya.
Ta bayyana cewa daga yanzu lambar loda katin waya ita ce *311*lambar katin sannan#.
Ga jerin gajerun lambobin da amfaninsu:
300 – Kiran cibiyar hulda da jama’a.
301 – Tura sakon murya.
302 – Bude sakon murya.
303 – Karbar rance.
305 – Ficewa daga tsari.
310 – Duba kati.
311 – Sanya kati.
312 – Tsarin data.
321 – Tura wa wasu.
323 – Duba data.
966 – Hada layi da katin dan kasa
2442 – Dakatar da sakonnin talla.
3232 – Sauya network.
Sanarwar da hukumar NCC ta fitar a ranar 13 ga watan Maris ta ce lambobin bai-dayan za su saukaka wa masu amfani da waya a Najeriya wahalar da a baya suke yi na rike lambobin kowane kamfanin sadarwa da suke amfani da layinsa.
Ta ce ta ba da wa’adin 17 ga watan Mayu ne domin kamfanonin sadarwa su samu sauye-sauyen da suka kamata.
Kawo yanzu dai babu wata sabuwar sanarwa daga hukumar ta NCC game da wannan batu.