Fiye da mutane 100 sun mutu cikin sa’o’i 48 a hare-haren jihar Plateau – Maren

0
87

 

Dan Majalisar tarayya da ke wakiltar Mangu da Bokkos Solomon Maren yayin jawabinsa gaban zaman zauren majalisar jiya laraba, ya ce mahara na ci gaba da kai hare-hare kan kauyuka tare da kisan mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Mr Maren, ya bayyana cewa hare-haren sun fi tsananta a yankin da ya ke wakilta a jihar ta Pulato da ke tsakiyar Najeriya wanda ke nuna bukatar daukar mataki lura da yadda mutanen kauyukan da ake kai hare-haren ke rayuwa cike da fargaba.

Dan Majalisar ya bayyana cewa cikin sa’o’I 48 sai da hare-haren ya kashe mutane fiye da 100 wanda ke nuna mutuwar mutanen da yawansu yah aura 200 a makamantan hare-haren cikin watanni 2 da suka gabata.

A cewar Mr Maren maharan na kone gidaje da gonaki har ma da shagunan da ake adana amfanin gona yana mai kakkausar suka ga matakan da gwamnati ke dauka a kokarin yaki da matsalar tsaron da yankuna da dama ke fama da shi a Najeriya.

Matsalar tsaro na ci gaba da ta’azzara a sassan Najeriya musamman yankin arewaci inda ‘yan bindiga ke kai hare-haren ba gaira babu dalili tare da kisan tarin mutane da kuma sace dukiyoyinsu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here