Newcastle da Manchester United na son sayen Sadio Mane daga Bayern Munich

0
105

Dan wasan mai shekaru 31 ya fuskanci gagarumin koma baya tun bayan komawarsa Bayern Munich ta Jamus daga Liverpool a farkon wannan kaka kan yuro miliyan 27 da rabi.

Wasu bayanai na nuna cewa mai horar da kungiyar ta Bayern Munich a shirye ya ke ya sayar da Mane lura da yadda kwalliya ta gaza biyan kudin sabulu game da cinikin nasa.

Kwallaye 12 kadai Mane ya iya zurawa tun bayan zuwansa Bayern Munich duk da yadda aka saye shi don maye gurbin Lewandowski da ke matsayin mafi zurawa kungiyar kwallo.

Mane dan Senegal mai shekaru 31 ya yi ta fama da jinyar rauni na tsawon watanni tun bayan komawarsa Bayern Munich daga Liverpool wanda ya hana masa damar fara taka leda da wuri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here