Rantsar da Tinubu: Za a kulle wasu ma’aikatu a Abuja tsawon kwana huɗu

0
117

Hukumomi a Najeriya za su hana shiga da fita a kewayen Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke tsakiyar birnin Abuja tsawon kwana huɗu saboda bikin rantsar da Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Kazalika, jami’an tsaro za su kulle ma’aikatar harkokin wajen ƙasar tun daga ranar Juma’a, 26 har zuwa Talata, 30 ga watan Mayu.

“Ba za a ƙyale ma’aikata da masu ziyara su shiga ma’aikatun ba har sai Talata, 30 ga wata. lokacin da za a ci gaba da ayyuka cikin gaggawa,” a cewar wata sanarwa da ofishin kula da ma’aikatan gwamnatin tarayya ya fitar a jiya Juma’a.

A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da Bola Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki, inda zai jagoranci ƙasar tsawon shekara huɗu bayan ya yi nasara a zaɓen watan Fabarairu da ya gabata.

Sai dai jam’iyyar PDP da ɗan takararta Atiku Abubakar na ƙalubalantar sakamakon zaɓen a kotu, suna masu cewa an tafka maguɗi. Ita ma Labour Party ta Peter Obi ta shigar da ƙara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here