An cimma jituwa tsakanin kungiyar likitoci da gwamnatin Najeriya

0
105

Akwai yiwuwar kungiyar likitocin Najeriya masu neman kwarewa ta janye yajin aikin da ta shiga nan da sa’o’i 48.

Jaridar The Nation da ake wallafawa a kasar ta ruwaito cewa an yi zaman sasanci tsakanin kungiyar da Ministan Kwadagon Najeriya Chris Ngige a jiya Juma’a. Sannan an rattaba hannu a yarjejeniyar fahimta tsakanin bangarorin biyu.

Kungiyar wadda bata ce komai ba game da janye yajin aikin, jaridar ta ce ta bukaci sai ta yi zama da majalisar zartaswanta kafin daukar matsaya game da komawa bakin aikin.

Yajin aikin gargadi wanda likitocin suka tsunduma a ranar 17 ga watan Mayun da muke ciki na tsawon kwanaki biyar, a ranar litinin ne wa’adin da suka baiwa gwamnatin kasar zai kare na neman a biya musu bukatunsu ko kuma su zarce da yajin aikin sai in mas ha Allah.

Daga cikin bukatun nasu, suna neman gwamnatin da ta musu karin albbashi da alawus-alawu, soke kuudirin dokar hana likitoci barin kasar da sunan aiki a kasashen waje bayan kammala karatu da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here