Liverpool za ta dauki Mac Allister, ana rububin Kimmich

0
112

Liverpool ta kusan kulla yarjejeniya da Brighton, domin daukar Alexis Mac Allister, har yanzu ba a kai ga cimma matsaya ba. (Fabrizio Romano)

Kociyan Brighton, Roberto de Zerbi ya bukaci mahukuntan kungiyar da kada su sayar da Kaoru Mitoma da Mac Allister da Moises Caicedo, wanda ake cewar zai bar kulub din a karshen kakar nan. (Football Insider)

Arsenal da Liverpool da kuma Barcelona na rige-rigen daukar dan kwallon Bayern Munich, Joshua Kimmich. (Marca – in Spanish)

Manchester City za ta yi wa Ilkay Gundogan tayin sabon kwantiragi mai tsoka da zai karkare a karshen Yunin 2024 da cewar za a yi kara masa kaka daya, wanda Barcelona ke so saya. (Fabrizio Romano)

Barcelona na bibiyar dan kwallon Manchester City, Joao Cancelo, wanda ke wasannin aro a Bayern Munich, wadda ke fatan tsawaita zamansa a Jamus. (Mundo Deportivo – in Spanish)

Newcastle United na kan gaba a kokarin sayen dan wasan Arsenal, Kieran Tierney a karshen kakar nan, wanda Manchester City da Aston Villa ke son dauka. (Football Insider)

A shirye West Ham take ta bar Gianluca Scamacca ya koma buga Serie A, shekara daya tsakani da ya koma taka leda a Premier League daga Sassuolo, wanda AC Milan ke sa ran yin zawarcinsa. (Gazzetta dello Sport – in Italian)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here