Hukumomin lafiya a Afirka ta kudu sun ce kwalara ta kashe aƙalla mutum 10 a Gauteng, yanki mafi yawan al’umma a ƙasar.
Haka nan mutune aƙalla 95 ne suka garzaya asibiti bisa alamomin kamuwa da cutar a yankin Hammanskraal da ke arewacin babban birnin ƙasar, Pretoria. Wata sanarwa ta ce ya zuwa ranar Lahadi an kwantar da mutum 37
. Waɗanda suka kamu sun haɗa har da ƙananan yara. Shugaban sashen lafiya na lardin, Nomantu Nkomo-Ralehoko ya buƙaci mutane da su ya taka-tsantsan tare da ɗaukan matakan kariya. A birnin Tshwane an gargaɗi mazauna yankin Hammanskraal da su guji shan ruwan famfo saboda kare kai, inda za a samar da wani ruwan shan na daban a tankuna.