Bayan shafe mako guda a gidan yari an saki Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi

0
122

Babban malamin addinin musulunci a jihar Bauchi, Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi, ya samu fitowa daga gidan yari bayan shafe tsawon kwanaki har bakwai a tsare bisa zarginsa da ake yi da tada zaune tsaye da ke barazana ga zaman lafiyan jihar Bauchi.

Idris wanda shi ne babban limamin masallaci na Dutsen Tanshi da ke Bauchi ya fito daga gidan yari ne a yau Litinin.

Idan za ku tuna dai Kotu ta aike da Idris Dutsen Tanshi gidan yari bisa zarginsa kalaman tada zaune tsaye da ke barazana ga zaman lafiya.

Malamin wanda ya amsa gayyatar ‘yansanda a ranar Litinin makon jiya daga bisani suka gurfanar da shi a gaban kotun majistire ta 1 da ke Bauchi bisa zargin tada zaune tsaye.

Kotun dai ta bayar da belinsa a ranar Talata bisa sharadin zai kawo Hakimi, babban Sakataren da ke aiki a karkashin Gwamnatin jihar Bauchi da kuma wani babban malamin da za su tsaya masa domin karbar belinsa. Kodayake an tafka muhawara kafin daga bisani malamin ya iya cika wadannan sharudan.

Da yake tabbatar da fitowar malamin, Shugaban kungiyar, Majalisar Matasa Masu Neman Hadin Kan Malamai Da Cigaban Al’ummar Jihar Bauchi, Yusuf A. Jibrin, ya shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa, “Yanzu haka Muna tare da Malam a masallacinsa yana kokarin yin sallar Azahar. Da safe mun je kotu aka sako Malam muka wuce kotu aka cike ka’idojin da suka dace yanzu haka Malam ya samu cikakken ‘yancinsa.”

Ya kuma tabbatar mana da cewa malamin ya cika ka’idojin da ake bukata na fitowarsa..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here