Ganduje ya rushe majalisar zartarwarsa

0
90

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da umarni ga dukkanin Kwamishinoni da shugabannin Ma’aikatu da hukumomin gwamnatin Kano da su ajiye mukamansu nan da kawana hudu.

Kadaura24 ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ofishin sakataren gwamnatin Kano ya fitar mai dauke da sa hannun babbar sakatariyar ofishin Bilkisu Shehu Maimota.

Sanarwar ta kuma bukaci masu mukaman Siyasa da su mika ragamar ma’aikatunsu ga manyan Sakatarorin gwamnatin ko daraktoci ma’aikatunsu tare da kayan gwamnati dake wurinsu.

”Wadanda mukamin da aka basu yana da wa’adin sauka to su cigaba da rike mukamansu dai-dai da yadda dokokin da suka nada su suka tanada”. A cewar sanarwar

Sanarwar ta godewa daukacin wadanda suka rike mukaman saboda irin gudunmawar da suka baiwa gwamnatinsa da kuma irin nasarorin da ya samu tsahon shekaru 8 da suka gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here