Tony Blair ya ziyarci Tinubu a Abuja

0
149

Tsohon Firaministan Birtaniya, Tony Blair ya ziyarci zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a Abuja a ranar Talata.

Wata sanarwa da ofishin zababben shugaban kasar ya fitar ta bayyana cewa, Cibiyar Tony Blair mai rajin kawo sauyi a tsarin gudanarwa ta duniya za ta kulla kawance da gwamnatin Tinubu musamman wajen ba da shawarwari wajen aiwatar da kyawawan manufofin gwamnatin.

Tony Blair ya kara da cewa “Tun da ya bar ofis a matsayin Firaministan Birtaniya, yana aiki tare da gwamnatoci na duniya don taimaka musu wajen aiwatar da ayyukansu managarta.”

“Muna so mu taimaka ta kowace hanya a gwamnatinku. Mu kawai muna bukatar mu san kudurorin gwamnatinku sannan mu kuma za mu taimaka wajen aiwatar da kudurorin.” Blair ya shaida wa zababben shugaban kasa Tinubu.

Blair ya amince cewa, lallai akwai aiki mawuyaci a gaban shugabannin kasashen duniya na wannan zamani a daidai lokacin da duniya ke cikin rudani.

A cewar sanarwar, Tinubu ya nuna jin dadinsa ga Blair kan ziyarar da ya kawo masa da kuma tayin aiki da gwamnatinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here