Gwamna Ganduje ya mika rahoton mika mulki ga Abba Gida-gida

0
125

Gwamnan jihar Kano mai barin gado Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da rahoton mika mulki ga zababben gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf Gida-gida.

A wata ‘yar gajeriyar ganawa da aka yi a dakin taro na gidan gwamnatin Kano, Ganduje wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman ya jaddada aniyarsa na ganin an mika mulki ranar 29 ga watan Mayun 2023 batare da wata takaddama ba.

Ya bukaci gwamnati mai jiran gado da ta yi nazari kan rahoton tare da bayar da ra’ayoyinsu a inda ya dace, sannan kuma sakataren ya yaba wa kwamitin mika mulki na gwamnati mai barin gado kan bajintar da suka nuna musamman ta yadda suka samar da kofin rahoton har gida Uku wanda ya tattaro duka sassan jihar.

A nasa jawabin, zababben gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, shi ma wanda ya samu wakilci daga shugaban kwamitin mika mulki na jam’iyyar NNPP Dakta Abdullahi Baffa Bichi, ya bayyana cewa kwamitin nasa zai kai rahoto ga gwamna mai jiran gado sannan zai dawo da rahoto in akwai inda ake da bukatar karin bayani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here