An dawo da wutar lantarki a wani asibiti da ke arewacin kasar Ghana, abin da ya faranta wa wani likita rai wanda ya ce jarirai biyu sun rasu bayan kamfanin wutar lantaki na gwamnati ya yanke wa asibitin wuta a farkon watan nan.
Dr Gbeadese Ahmed wanda ke asibitin St Anne da ke Damango, ya shaida wa BBC cewa ya na shirin komawa tiyata domin ya cigaba da ayyukan da aka dakatar na tsawon kwanaki bakwai.
Ya ce, É—an majalisar yankin wanda kuma minista ne a gwamnati, Abdulai Jinapur ya biya wasu basuskan da kamfanin wutar lantarkin ta Nedco ke bin asibitin.
Agajin da É—an siyasar ya kawo ya biyo bayan tattaunawa da Dr Ahmed ya yi da tashar Citi news ranar Liltinin a kan yadda yanke wutar lantarkin ya sanya asibitin cikin mawuyacin hali a garin wanda ke da nisa kilomita 630 daga babbn birnin kasar, Accra.
Ya yi bayanin cewa jarirai biyu sun rasu kuma wasu jarirai uku na cikin mawuyacin hali saboda rashin wutar ya hana ma’aikatan asibitin yi wa jariran Æ™arin jini.
An fara samun matsala a asibitin ne a ranar 4 ga watan Mayu lokacin da aka fara yanke wutar sakamakon bashin sama da $370, 000 da ake bin ta.
A lokacin ne jaririn farko ya rasu, a cewar Dr Ahmed.
An dawo da wutar lantarkin amma hukumar kamfanin Nedco sun yi gargaÉ—in cewa za a sake yankewa idan har ba a biya ta duka bashin da ta ke bi ba- kuma hakan ya faru a ranar 16 ga watan Mayu.
Jariri na biyu ya rasu cikin makon da ya gabata.
Tun farkon watan Mayu kamfanonin rarraba wutar lantarki na Ghana suka fara matsa lamba kan marasa biyan kuɗin wuta a ƙoƙarin da su ke yi na karbo miliyoyin kuɗi da su ke bi bashi.
An yanke wa ma’aikatun gwamnati da dama wuta sakamakon rashin biyan kuÉ—in wutar lantarki.