Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno mai ritaya, ya ce babu wani dalilin da zai sa ya yi nadama kan yadda ya gudanar da aikinsa ko da kuwa matakan da ya ɗauka ba su yi wasu mutane daɗi ba.
A wata hirar da ya yi da BBC Hausa, Janar Monguno ya ce babban ƙalubalen da ya fuskanta shi ne taƙaddamar da ya rinƙa yi da mutane da kuma kungiyoyi kan matakan da ya ɗauka musamman kan hana shigowa da miyagun abubuwa Najeriya.
“Da na zo sai na ce babu wanda zai laɓe karkashin ma’aikatana su sami waɗannan abubuwan, wannan abin ya tayar wa mutane da yawa hankali amma ba abin da zai sa in yi nadama ba ne. An yaƙe ni ƙwarai da gaske.” A cewarsa.
Janar Monguno, ya ce cikin shekaru biyu da suka wuce, ofishinsa ya yi iyakacin ƙoƙarinsa wurin yaƙi da yaɗuwar ƙananan makamai a inda ya buƙaci haɗin kan al’umma wurin samun bayanai da za su taimaka wajen hana shigowa da makaman.