Ba mu da masaniya kan ayyukan dakarun Birtaniya a Najeriya -Babagana Monguno

0
102

Babagana Munguna ya kuma yi bayani kan batun da ake yi na cewa dakarun wasu ƙasashen ƙetare sun gudanar da wasu abubuwa a Najeriya.

Ya ce ba shi da wata masaniya kan labarin da ke cewa sojojin Birtaniya na musamman sun kai kusan shekaru goma suna aiki a asirce a cikin Najeriya.

A ranar Talatar da ta wuce wata jaridar Birtaniya ta fitar da wani rahoto cewa dakaru na musamman da aka fi sani da SAS na aiki a asirce a kasashe 19 ciki har da Najeriya tun shekara ta 2011.

Janar Munguno ya bayar da tabbacin cewa rahoto mai kama da wannan bai iso gare shi ba “Ni ban da wannan labarin domin bai zo ofishina ba, ƙila waɗansu jami’an sun samu amma babu wanda ya kawo min” a cewar sa.

Cikin shekara takwas da ya yi tare da shugaba Buhari, ya bayyana cewa ya bai wa shugaban ƙasar shawarwari da dama waɗanda suka yi tasiri wurin inganta mu’amullar Najeriya da sauran ƙasashe, tare da kawo cigaba a yaƙin da ake yi da matsalar rashin tsaro a cikin gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here