Bama bukatar dukiyar Najeriya domin mu rayu – Remi Tinubu

0
113

Uwargidan zababben shugaban Najeriya Oluremi Tinubu, ta ce ita da iyalanta basa bukatar dukiyar da kasar ta mallaka domin rayuwa, saboda wadatar da suke da ita. 

Yayin da take jawabin a wajen addu’oin da aka gudanar domin zuwar sabuwar gwamnati a mujami’ar Abuja, Remi Tinubu ta ce Allah Ya wadata su da abinda suke bukata kuma suna masu gode masa, saboda haka basa tunanin yin amfani da shugabancin Najeriya domin azurta Kansu da kudaden talakawa.

Uwargidan sabon shugaban ta ce itace zata zama matar shugaban kasa mafi yawan shekaru da zata shiga fadar shugaban kasa, ganin shekarun ta sun kai 63, yayin da mai gidanta ke da shekaru 71.

Tinubu tace suna bukatar taimakon Ubangiji domin hada kan jama’ar Najeriya da zummar samarwar kasar ci gaban da take bukata domin ci gaba da jagorancin nahiyar Afirka.

Uwargidan shugaban kasar tace kowanne ‘dan Najeriya yana da hakki akan dukiyar da kasar ta mallaka, kuma za suyi iya bakin kokarinsu wajen ganin anyi adalci ga kowanne ‘dan kasa domin dawo da Najeriya akan turba mai kyau.

Daga karshe ta bukaci addu’oin ‘yan Najeriya domin sauke nauyin shugabancin da aka dora musu. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here