Gwamnan jihar Kano mai barin gado, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, zai gudanar da mika ragamar mulkin jihar a hukumance ga zababben gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida mai barin gado, Malam Muhammad Garba ya fitar, ya bayyana cewa za a gabatar da taron ne da misalin karfe 9:00 na daren ranar Lahadi 28 ga watan Mayu a gidan gwamnatin Kano.
Ya ce tuni kwamitin rikon kwarya na gwamnatin jihar Kano ya sanar da hakan ga kwamitin mika mulki na zababben gwamnan.
Malam Garba ya ce, kwamitocin biyu sun gana cikin makon da ya gabata inda aka gabatar wa da kwamitin kundin mika ragamar mulki.
Kwamishinan ya bayyana cewa Gwamna Ganduje zai tafi Abuja a matsayin shugaban tawagar Kano don halartar rantsar da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.
Ya ce tafiyar ta gwamnan ta zama tilas gabanin rufe filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja domin halartar bikin rantsuwar.
Sanarwar ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da yi wa jihar Kano addu’ar zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.