Gwamnatin Kano ta ce kwacen waya daidai ya ke da fashi da makami

0
80

Majalisar tsaro a jihar kano ya aiyana kwacen wayar hannu a matsayin fashi da makami  tare da tabbatar da cewar duk wani ko wata tawagar mutane da aka samu da aikata wannan danyen aiki hukuncin fashi da makami za’a zartas a kansa.

A ‘yan makonnin da suka gabata batun kwacen wayar  hannun ya zama ruwan dare dama duniya a birnin na Kano, yayin da jami’an yansanda suka kama sama da mutane casa’in da ake zargi da aikata danyen aikin wasu goma kuma suka rasa rayukansu sanadiyar kwacen wayar.

Mazauna a birnin na kokawa dangane da yadda ake sakin barayin wayar bayan an kamasu kuma aka damka su a hannun jami’an tsaro domin bayan wasu ‘yan lokuta sai a ga sun fito suna yawo a cikin gari, wanda yin hakan kan zama barazana ga rayuwar al’uma.

Sai dai a wata sanarwa, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba ya ce majalisar tsaron da gwamna mai barin gado Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta a lokacin zamanta ta nuna rashin jin dadin ta, ta kuma lura da cewa an tafka wannan aika-aika a jihar.

Majalisar ta cigaba da cewa bisa wannan yasa aka mayar hukuncin laifin ya zama na fashi da makami domin suma kisa suke yi da jikkata mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here