Muhimman bangarori 8 da ke bukatar daukin gaggawa daga Tinubu

0
125

A yayin da gata Litinin, 29 ga Mayun ne za a rantsar da sabuwar gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda zai karbi mulki daga shugaban kasa Muhammadu Buhari, kwararru da masu ruwa-da-tsaki a muhimman sassan kasar nan sun nuna Shugaban Kasar na 16 alkiblar da ya kamata ya bi don kaiwa ga nasara.

Mutanen kasar nan na haba-haba Tinubu ya karbi mulki saboda alkawuran da ya dauka na magance dimbin matsalolin da suke addabar kasar nan.

Muhimman matsalolin da kwararru suka ce suna bukatar daukin gaggawa daga Tinubu sun hada da tsaro da tattalin arziki da lantarki/makamashi da hanyoyi da kiwon lafiya da ilimi da kuma noma.

Tsaro

Babban abin da masana suna bukaci Tinubu ya fara magancewa shi ne rashin tsaro, wanda ya kunshi ta’asar ’yan bindiga da garkuwa da mutane da ta’addanci da satar mai da yunkurin ballewa daga kasa da fadace-fadacen ’yan kungiyoyin asiri da rikicin manoma da makiyaya da rikicin kabilanci da damfarar Intanet da sauransu.

Kowace daga cikin shiyyoyin siyasa shida na kasar nan na fama da irin tata matsalar tsaron duk da tsoma sojoji a cikin lamarin a tsawon shekaru.

Misali wasu jihohi a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya suna fama da masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga, yayin da Neja-Delta ke fama da barayin mai. Sannan bincike ya nuna har yanzu ’yan ta’adda na tafka barna a Arewa maso Gabas.

Cire tallafin mai da matsalar wutar lantarki

Cire tallafin man fetur da rage farashi ko kara kudinsa na cikin manyan matsalolin da suke jiran Tinubu.

Yanzu dai ana sayar da lita daya a kan Naira 190. Gwamnatin Buhari ta kasa cire tallafi A bangaren wutar lantarki wajibi ne sabon Shugaban kasar ya nemo hanyar kara karfin wutar lantarki zuwa sama da megawatt 4,500 da aka fi samu a kasar nan wanda hakan ke kawo karanci da ingancin wutar lantarki.

Gwamnatin Buhari a bayan nan ta fadada wani kwamiti don ya kunshi wakilan gwamnati mai zuwa kan batun cire tallafin mai a bayan Yuni mai zuwa waa daya bayan Tinubu ya karbi mulki. Gwamnatin Buhar ta ce ta kashe Naira tiriliyan shida kan bayar da tallafi a cikin wata 18, amma duk da haka ’yan Najeriya na fama da wahalar mai a sama da shekara daya.

Masana sun ce abu ne mai wahala ga Tinubu ya ci gaba da bayar da tallafin alhali bai bayar da cikakken ’yanci ga bangaren fetur ba, inda a yanzu Kamfanin NNPC ne kadai yake shigo da mai.

Sai dai akwai yiwuwar bude matatar dangote ta rage radadin da ake sha a fannin mai, bisa sa ran NNPC zai rika sayen man daga matatar maimakon kasashen waje.

Bashin Naira tiriliyan 77

Wani babban kalubalen da Tinubu zai fuskanta shi ne na adadin bashin da ake bin Najeriya a ciki da wajenta wanda ya kai Naira tiriliyan77. 46.25 a cikin zango na 4 a bara, kuma bashin ya karu daga Naira tiriliyan 44.06 daga zango na 3 a bara, kamar yadda Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar a rahotonta na kwata-kwata mai taken “Yawan bashin cikin gida da waje a karshen bara.

Sai dai a yanzu Majalisar Dokoki ta kasa ta amince a karbo bashin Naira tiriliyan 22 ta hannun Bankin CBN.

Kasafin Kudin 2023 kuma an yi shi ne da gibin kimanin Naira tiriliyan 10 wanda a karshe zai iya yin tashin gwauron zabo, ya ninka zuwa kusan Naira tiriliyan 77 idan sabuwar gwamnati ta zo.

A kwanakin baya Gwamnatin Tarayya ta aro Naira biliyan 366 daga Bankin Duniya don saukaka illar da cire tallafin mai zai haifar, wanda a yanzu aka dakatar da shi.

Kidayar jama’a

A kwanakin baya ne Shugaba Buhari ya amince da dage aikin kidayar 2023, wadda tun farko aka shirya gudanarwa a ranar 3 zuwa 7 ga Mayun nan, inda ya bar wa gwamnati mai jiran gado wuka da naman tantance ranar da za a gudanar da aikin.

Wata sanarwa da Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya fitar ta ce, Shugaban kasa ya amince da dage ranar ce bayan taron Majalisar Zartarwa da ganawa da Shugaban Hukumar kidaya ta kasa da ayarinsa a Abuja.

Hukumar NPC da ke gudanar da kidayar, ta tabbatar akwai sauran na’urori da take bukata don gudanar da aikin, inda ta ce nan da ’yan kwanaki za a sayo wasu na’urorin.

Don haka, sabon Shugaban kasa ne zai tantance lokacin da za a yi kidayar. Lokaci na karshe da aka yi kidayar jama’a a Najeriya shi ne a shekarar 2006, wanda ya nuna yawan al’ummar kasar nan ya kai miliyan 180.

Sai dai rahoton Yawan Jama’a na Majalisar dinkin Duniya ya kiyasta cewa, adadin al’ummar Najeriya zai haura miliyan 223.8 nan da tsakiyar shekarar 2023 daga miliyan 216 a shekarar 2022.

Sake fasalin Naira

A watan Oktoban 2022, CBN ya sanar da sake fasalin wasu takardun Naira. Babban Bankin ya sake fasalin takardun Naira 200 da 500 da kuma 1000, lamarin da ya jefa al’umma cikin wahalhalu.

Babban Bankin ya kudiri aniyar sake fasalin kudi ne kafin zaben Shugaban kasa na 2023, inda har ta kai dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar APC a lokacin, Bola Tinubu ya zargi wasu masu rike da madafun iko da amfani da sake fasalin Nairar da kuma karancin man fetur wajen kawo wa burinsa na son zama Shugaban Kasa cikas.

Duk da an kawo karshen matsalar, amma za a dauki tsawon lokaci ba manta ba.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne irin matakin da gwamnatin Tinubu za ta dauki a kan wa’adin ranar 31 ga Disamba na daina amfani da tsofaffin kudin kamar yadda Kotun Koli ta yanke hukunci.

Rashin aikin yi A cewar Hukumar kididdiga ta kasa, rashin aikin yi a Najeriya ya kai kashi 33 cikin 100.

Sai dai Kamfanin Binciken Kudi na KPMG ya ce, rashin aikin yi a Najeriya ya karu zuwa kashi 37.7 cikin 100 a shekarar 2022 kuma zai iya karuwa zuwa kashi 40.6 cikin 100, saboda karuwar da ake samu ta masu neman aiki.

Duk da cewa gwamnati mai ci ta bullo da tsare-tsare daban-daban na inganta kasuwanci da sana’o’in hannu, kamar shirin N-Power da shirin karfafa wa ’yan kasuwa da sauransu, babban tasirin da ake sa ran zai yi ga ci gaban tattalin arzikin bai taka kara ya karya ba.

Don haka, sabuwar gwamnati tana iya samar wa al’ummarta ayyukan yi cikin kankanin lokaci don rage radadin talauci da dakile shiga ayyukan manyan laifuka.

Inganta noma

kwararu a wananan fanni sun bayyana cewa, Shugaban kasa mai jiran gado yana bukatar ya mayar da hankali kan abubuwa shida da suka zama kalubale ga noma kuma suka hana harkar kaiwa ga ci a kasar nan.

Abubuwan da zai tunkara sun hada da shawo kan matsalar taki da kuma rikicin da ake yawan samu tsakanin manoma da makiyaya.

Haka kuma dole ne a samar wa manoma hanyar samun kudi da kuma kara inganta kayayyakin noman rani da samun karuwar kayan aikin gona na zamani.

Manoma da masu ruwa da tsaki sun amince cewa, wadanan abubuwa su ne suka zame wa ci gaban ayyukan gona tarnaki tare da mayanr da hannun agogo baya.

Kabiru Ibrahim shi ne Shugaban kungiyar Manoma ta kasa AFAN ya bayyana cewa, akwai bukatar a karfafa wa manoma gwiwa kan yin noma a gabadayan shekara ta hanyar zuba jari a harkar noman rani da kuma samar da kayan aikin noman.

Ta haka ne kawai gwmanati mai jiran gado za ta samu kai wa gaci a bangaren aikin gona.

“Ya kamata gwamnati mai shigowa ta mayar da hankali wajen gano irin karfi da kuma abin da kowane yanki na fadin kasar nan zai iya samarwa. Haka kuma ta yi kokarin rage musu kudin duk wasu kayayaykin noma da suke bukata”

Dukkanin kabilun da ke yankuna shida na fadin kasar nan ya kamata su zauna su kimanta kawunansu don gano hanyar da za su bi wajen ganin an rika samar da kayyayakin aikin noma.

Hakan zai sa manoma su san ana yi da su a shekarun farko an mulkinsa.

Shi ma a nasa jawabin, Shugaban kungiyar Manoman Dankali ta Kasa Cif Dan Okafor ya bayyana cewa, akwai bukatar gwamnatin ta mayar da hankali kan harkar tsaro da wutar lantarki da harkar noman rani da samar da hanyoyi a karkara da samar da tsarin inshora ga manoma.

Shi kuwa wani masanin tattalin arziki mai suna Mista Dele Adebisi ya bayayan cewa, dole gwamnati mai zuwa ta duba hanyoyin da za a tabbatar cewa manoma sun samu kayan noma, inda ya ce samuwar isassun kayan aiki zai janyo raguwar kudin da ake kashewa a harka noma.

Aikin titin Kaduna zuwa Abuja

Wani muhimmin aiki shi ne aikin Kaduna zuwa Abuja, wanda asali ya fara ne daga Abuja zuwa Kano. A ranar Talata da ta gabata ce Shugaba Buhari ya kaddamar da bangaren aikin na Kaduna zuwa Kano, inda ya gadar da karasa aikin na Kaduna zuwa Abuja ga sabuwar gwamnati.

Aminiya ta ruwaito cewa, aikin na tafiya sosai a hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda a kusan kullum ma’aikan suke aiki ba-ji-ba gani.

Titin jirgin kasan Kaduna zuwa Kano

A watan Yulin 2021 ne aka kaddamar da aikin titin jirgin daga Kaduna zuwa Kano, sannan akwai bangaren aikin titin jirgin kasan Abuja-Kaduna-Kano da ba a kammala ba.

Shi ma wannan aikin yana cikin ayyukan da ke bukatar kulawar gaggawar sabuwar gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here