Mamallakin tashar talabijin ta AIT ya rasu

0
108

Gogagge dan jarida kuma shugaban kamfanin sadarwa na DAAR communication da gidan Talebijin na AIT da Radiyon Raypower, High Chief Raymond Aleogho Anthony Dokpesi, ya kwanta dama.

Dokpesi ya rasu a ranar Litinin 29 ga watan Mayun 2023.

An bayyana rasuwar marigayin a wata sanarwa da iyalansa suka fitar dauke da sanya hannun babban dansa, Raymond Dokpesi (JNR).

Iyalan marigayin sun misalta shi a matsayin jigo, Uba kuma aboki ga dubban jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here