Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya janye tallafin man fetur.
Tinubu ya ce tallafin mai ya zama tarihi ne jim kadan bayan an ranstar da shi a Dandalin Eagle Square da ke Abuja.
Ya ce biyan tallafin abu ne ba mai dorewa ba, don haka gara a yi amfani da kudaden da ake kashewa wajen biyan tallafin domin yin wasu ayyukan raya kasa.