Tsohon shugaban Kasa Buhari ya sauya sunayen filayen jiragen sama 15 awanni kafin yabar mulki

0
132

Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a wani mataki na karshen mulkinsa da ya dauka, kafin rantsar da sabon shugaban kasaya amince da canza sunan wasu filayen jirgin sama guda 15 ga sunayen wasu fitattu kuma shahararrun ‘yan Nijeriya.

 

A cewar kakakin ma’aikatar kula da sufurin jiragen Sama, Odutayo Oluseyi, ta cikin sanarwar da ya fitar a safiyar ranar Litinin, ya ce filayen sauka da tashin jiragen sun had da filin sauka da tashin jiragen Sama na kasa da kasa ta Akure da aka canza zuwa sunan Olumuyiwa Bernard Aliu; da filin sauka da tashin jiragen Sama na kasa da kasa ta Benin da yanzu ta koma filin jirgin Oba Akenzua II.

Sauran sun hada da filin sauka da tashin jiragen Sama na kasa da kasa ta Dutse da yanzu aka canza zuwa sunan Muhammed Nuhu Sanusi;

filin sauka da tashin jiragen Sama na kasa da kasa ta Ebonyi zuwa Chuba Wilberforce Okadigbo; da filin sauka da tashin jiragen Sama na kasa da kasa ta Gombe da aka sauya zuwa sunan Burgediya Zakari Maimalari.

 

 

Ma’aikatar ta kuma sauya sunan filin sauka da tashin jiragen Sama na kasa da kasa ta Ibadan zuwa sunan Samuel Ladoke Akintola; filin sauka da tashin jiragen Sama na kasa da kasa ta Ilorin zuwa sunan Janar Tunde Abdullahi Idiagbon; filin sauka da tashin jiragen Sama na kasa da kasa ta Kaduna zuwa sunan Janar Hassan Usman Katsina, da kuma filin sauka da tashin jiragen Sama na kasa da kasa ta Maiduguri zuwa sunan shugaba Muhammadu Buhari.

 

 

Sauran sun ne: filin sauka da tashin jiragen Sama na kasa da kasa ta Makurdi zuwa sunan Joseph Sarwuan Tarka; filin sauka da tashin jiragen Sama na kasa da kasa ta Minna zuwa sunan Mallam Abubakar Imam; filin sauka da tashin jiragen Sama na kasa da kasa ta Nasarrawa zuwa suna tunawa da Shehu Usman Danfodio; filin sauka da tashin jiragen Sama na kasa da kasa ta Osubi zuwa sunan Alfred Diete Spiff; filin sauka da tashin jiragen Sama na kasa da kasa ta Port Harcourt zuwa sunan Obafemi Jeremiah Awolowo da kuma filin sauka da tashin jiragen Sama na kasa da kasa ta Yola zuwa sunan Lamido Aliyu Mustapha

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here